✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda magoya bayan APC suka tarbi Gawuna a Kano

Wannan ita ce ziyarar Gawuna ta farko tun bayan da APC ta fadi zaben gwamnan jihar.

Magoya bayan jam’iyyar APC a Jihar Kano, sun tarbi dan takarar Gwamna na jam’iyyar a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna a jihar.

Wannan dai ita ce, ziyarar Gawuna ta farko da ya kai jihar tun bayan da jam’iyyarsa ta APC ta fadi zaben gwamnan jihar.

Idan za a tuna, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci jihar bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, wanda ya sa jam’iyyar ta yi rashin nasara.

Magoya bayan jam’iyyar sun tarbi Gawuna a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, inda suka raka shi zuwa gidansa da ke Miller road.

Wata majiya ta ce, Gawuna ya je jihar ne domin ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki da kuma gaisawa da magoya bayan jam’iyyar da dai sauransu.

Ga hotunan yadda aka tarbe shi: