✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zanga-zangar tsadar rayuwa ke gudana a Najeriya

Farashin kayan masarufi sun ninninku, sannan gwamnatin ba ta cika alkawarin da ta yi na karin albashi da kuma tallafi ba

A yau ne kungiyoyin kwadago a fadin Najeriya suke gudanar da zanga-zanga saboda tsadar rayuwa da kasar ke fama da ita a sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi da kuma faduwar darajar Naira.

A halin a ake ciki farashin kayan masarufi sun ninninku a kasar, sannan har yanzu  gwamnatin ba ta cika alkawarin da ta yi na karin albashi da kuma tallafin abinci da sauransu domin rage wa ’yan kasar radadin tsadar rayuwa da ke ci gaba da addabar su ba.

Ga hotunan yadda zanga-zangar ke gudana, daga wakilanmu.