✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar EFCC ta tsare Doyin Okupe

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta tsare tsohon mai taimaka wa shugaba Jonathan a kan harkokin yada…

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta tsare tsohon mai taimaka wa shugaba Jonathan a kan harkokin yada labarai Dakta Doyin Okupe a ofishinsu inda a yanzu yake tsare kwana biyu a hannun hukumar.

A cewar mukaddashin kakakin hukumar EFCC Tony Orilade, ya ce EFCC ta tsare Okupe ne don ya amsa wasu tambayoyi da ake bukata daga wurinsa, wadanda suke da alaka da harkokin kudade na ofishinsa lokacin da yake rike da mukamin gwamnati.