✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahim Isa Na BBC Ya Zama Shugaban Kafar Yada Labaran Jihar Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya nada Ibrahim Isa na Sashen Hausa na BBC a matsayin Babban Daraktan Kafar Yada Labarai na jihar…

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya nada Ibrahim Isa na Sashen Hausa na BBC a matsayin Babban Daraktan Kafar Yada Labarai na jihar Gombe (GMC).

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya sanar ta hannun Babban Daraktan Yada Labarai na gidan gwamnatin jihar, Isma’ila Uba Misilli a yammacin ranar Litinin.

A cewar sanarwar, kwarewar Ibrahim Isa a aikin jarida ta sa aka ba shi muƙamin kuma aikinsa ya fara nan take daga nada shi.

Ibrahim Isa, ya share sama da shekaru 20 yana aikin jarida a sashen Hausa na BBC kafin ba shi wannan matsayi.

Kwararre ne a bangaren shirye-shirye da gabatarwa da karanta labarai, wanda ake ganin kwarewar tasa za ta kawo ci gaba mai ma’ana wa Gidan Rediyo da Talabijin mallakar jihar.

Sanarwar ta bayyana kwarin guiwar jagorancin Ibrahim Isa zai kawo ci gaba ga GMC kuma ya zo ne a lokacin da zai bayar da gudumawa wajen ciyar da harkar yada labarai gaba.

Ibrahim Isa dai kafin fara aikinsa a BBC, tsohon m’aikacin gidan Radiyo da Talabijin na jihar Gombe ne.