✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan mace tana kiyo…

Shin ya halatta a Musulunci mace ta ki biya wa mijinta bukatar aure?

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa amin.

Ga ci gaban amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.

Hukuncin mace mai kiyo

Tambaya: Miji yana da hakki ya nemi biyan bukatarsa a wajen matarsa in ba ta da wani uzuri?

Shin ya halatta a Musulunci mace ta ki biya wa mijinta bukatar aure ko da ba ta da wani uzuri?

Amsa: Yana da hakki ya nemi bukatarsa a kan matarsa amma ba ta karfi da duka da ji mata ciwo ba sai dai ta lalami da nasiha da sauran dubarun da suka dace.

In ta ki sai a zartar da mata da hanyoyin ladabtarwa wadanda shari’a ta tanada.

Bai halatta ba mace ta hana mijinta hakkin ibadar aure ba tare da wani uzuri, ko ma da uzurin, ta daure ta biya wa mijinta bukatarsa ya fi mata duniya da Lahira.

Hana miji hakkinsa na ibadar aure ba tare da wani uzuri ba babban alkaba’iri ne kuma zai sanya duk wacce ta aikata hakan ta kwana cikin fushin Allah Madaukakin Sarki.

Da wahalar Lahira…

Ga mata masu irin wannan dabi’a ta kin ibadar aure ga mazansu da farko ina son ku san cewa wannan tsananin wawanci ne gare ku.

Ko ma mene ne dalilin da ya sa ku aikata haka din, domin kun zabi jin dadin duniya sama da na ran gobe Kiyama, kun kwammace ku ji kunyar Lahira a kan ku ji ta duniya, to wannan kuwa wawanci ne na karshe, domin duk zaman me muke yi a nan duniyar in ba zaman jiran tafiya Lahirar ba?

To kuma ga shi an ce bin miji shi ne hanyar tsira ranar gobe Kiyama, to duk wadda take wasa da hanyarta ta tsira ranar gobe Kiyama kuwa ba karamar marar wayo ba ce.

Girman miji a wajen matarsa bai da iyaka. Uwar Muminai A’ishatu (RA) ta yi mana wannan kiran: “Ya ku mata! In da kun san girman hakkin da mazanku suke da shi a kanku, lallai da kowacenku ta share daudar tafin kafar mijinta da fuskarta!”

Sannan Annabi (SAW) ya tambayi wata sahabiya ya ce: “Yaya kike da mijinki?” Sai ta ce, “Ina iyakar kokarina gare shi, sai dai a kan abubuwan da suka fi karfina.” Sai ya ce, “Ki kula sosai da yadda kika mu’amalance shi domin shi aljannarki ne!”

Duk macen da mijinta ya kira ta shimfidar barcinsu ta ki zuwa, mala’iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari.

To ko mala’ika daya ya tsine wa mutum ya iya da haka?

Ku ji fa yadda tsinuwar uwa take yin tasiri ga rayuwar da, to ina kuma ga tsinuwar mala’iku su da ba su taba sabon Allah ba?

Haka nan duk matar da mijinta ya yi fushi da ita wanda ke sama (SWT) zai yi fushi da ita har sai mijinta ya bar fushi da ita, kuma duk ibadunta ba a amsarsu har sai mijinta ya daina fushi da ita.

Allah (SWT) Yana tabbatar da tsinuwarSa ga macen da idan mijinta ya kiraye ta don ibadar aure takan tsaya ta bata lokaci har sai da barci ya kwashe mijin.

Haka kuma Annabi (SAW) ya yi umarni da cewa: “In miji ya kirayi matarsa (domin ibadar aure) ta zo ko da tana bisa rakumi ne.

“A wani wajen kuma ko da tana gindin murhun girki ne.”

Da wahalar Lahira dai, gara ta duniya komai tsananinta.

Da fatar kunnenku ya ji muku jin da zai tsirar da jikinku daga wuta, amin!

Sai mako na gaba insha Allah. Da fatar Allah Ya sa mu kasance a cikin kulawarsa a koyaushe, amin.