✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan Sudan ta biya kudi zan cire ta daga jerin ‘yan ta’adda – Trump

Da zarar ta biya kudin, to zan cire ta daga jerin kasashen da ke daukar nauyin ta’addanci a duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasarsa za ta cire Sudan daga jerin kasashen da ke daukar nauyin ta’addanci a duniya bayan Sudan din ta amince da yarjejeniyar biyan diyyar miliyoyin daloli ga iyalan Amurkawa da wadanda hare-haren ta’addancin ya shafa.

Shugaba Trump ya wallafa a Twitter cewa: “BABBAN labari! Sabuwar gwamnatin Sudan, wacce take samar da muhimmin ci gaba, ta yarda ta biya Dala miliyan 335 ga iyalai da Amurkawan da ta’addanci ya shafa.

Da zarar ta biya kudin, to zan cire Sudan daga jerin kasashen da ke daukar nauyin ta’addanci a duniya.

A karshe an yi ADALCI ga Amurkawa kuma muhimmin mataki ga Sudan!”

Matakin zai ba Sudan damar komawa karbar rance da tallafin kasashen duniya wanda kasar ke matukar bukata wajen habaka tattalin arzikinta.

Zai kuma bude kofa ga kasar wajen kulla dangantakar diflomasiyya da Isra’ila, yayin da gwamnatin Trump ke kokarin kulla kawancen da kasashen Larabawa su amince da wanzuwar kasar Isra’ila.

Gwamnatin Trump ta hada makamanciyar yarjejeniyar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain.

Firayi Ministan Sudan, Abdalla Hamdok ya yi godiya ga Trump inda ya ce saka Sudan a jerin masu daukar nauyin ta’addanci ya yi matukar illa ga kasar.

Sa’annan ya ce al’ummar Sudan ba su taba mara wa ta’addanci baya ba, kuma yunkurin na Amurka wani muhimmin goyon baya ne ga Sudan wajen komawarta turbar dimokuradiyya.

Dala miliyan 335 da Sudan ta amince ta biya ga Amurkawan da hare-haren ta’addancin Alka’ida ya shafa ne a ofisoshin jakadancin Amurkar da ke a Kenya da Tanzaniya a 1998 da kuma harin bam kan jirgin ruwanta mai suna USS Cole a 2000 a tashar ruwan Yemen.

Kotunan Amurkar sun samu Sudan da hannu a hare-haren.