Ina aka tsaya bayan cire Sarkin Maru? | Aminiya

Ina aka tsaya bayan cire Sarkin Maru?

Ina taya Aminiya murnar shiga sabuwar shekarar 2020.

Sannan ina kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara kan kalubalen da take ciki, na yin hukunci ga sauran masu fada-a-ji da ake zargi da hannu a kan sha’anin tashin hankalin da ya addabi jihar. Abin da muke tsoro shi ne, kada a ce an cire Mai martaba Sarkin Maru ne a matsayin samfuri don saura su ji tsoro. Kamar yadda tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ahmad Sani ya sa aka yanke wa wani hannu a matsayin samfuri ba tare da dorewar abin ba. Yanzu haka sakamako na nan yana jiran Gwamna Bello Matawalle wajen ’yan majalisarsa domin ganin me zai yi a kai.

Daga Abdulkarim Muhammad Sulaiman Maru, Jihar Zamfara

08085995859