✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina da nasaba da Najeriya —Gimbiya Meghan

Gimbiya Meghan Markle da Yarima Harry sun ziyarci wasu kasashen Afirka a bana.

Sirikar Sarki Charles III, Meghan Markle ta ce wani bincike da ta gudanar ya tabbatar mata da cewa tana da nasaba da Najeriya ta wajen kakanni.

Uwar gidan Yarima Harry a wata hira ta musamman da ta yi da Spotify, ta ce binciken kwayoyin halitta da aka mata shekaru da suka gabata, an tabbatar mata da cewa tana da jinin Najeriya a jikinta da kusan kashi 43 cikin 100.

Sai dai ko da aka tambaye ta daga wacce kabila take a Najeriyar, ta ce bata da masaniya a kai, amma za ta fara bincikawa nan ba da jimawa ba.

A baya-bayan nan ne dai Gimbiya Meghan ta bayyana cewa tana da jini biyu a jikinta, amma ba ta yi cikakken bayan kan asalin nata ba.

A shekarar 2015 ne Mujallar ELLE ta wallafa labarin Gimbiya Meghan game da asalinta na ruwa biyu.

A watan Satumba na 2019, Gimbiyar ta yi jawabi ga asalinta na launin fata a karon farko tun lokacin da ta auri Duke na Sussex.

A cewar RFI, ma’auratan sun ziyarci wasu kasashen Afirka a wannan shekarar.