✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPMAN ta karyata batun kara kudin mai zuwa N700

IPMAN ta ce sam babu kamshin gaskiya a labarin

Kungiyar Dillalan Man Fetur da Najeriya (IPMAN), ta karyata labarin da ake yadawa cewa man fetur zai kai N700 kan kowacce lita.

Shugaban kungiyar na shiyyar Kudu maso Yamma, Alhaji Dele Tajudeen ne ya bayyana hakan a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Ibadan.

Ya kuma roki jama’a da su yi watsi da labarin sannan su daina rige-rigen sayen man suna boyewa.

Ya ce farashin da ake sayarwa a yanzu shi ne mafi kololuwa, kuma ba za a sayar da shi sama da hakan ba.

Alhaji Dele ya kuma jinjina wa Shugaban Kasa Bola Tinubu saboda cire tallafin man fetur din da ya yi.

“Hatta Dokar Man Fetur ta Kasa (PIA) ta fada karara cewa dole a cire tallafin. Saboda haka ina yaba masa saboda cire tallafin, kuma muna goyon bayansa 100 bisa 100, saboda yaudara ne kawai,” in ji shi.

Ya ce dan karin da aka samu a ’yan kwanakin nan an yi ne saboda karin kudin dakon man, amma mutane su tabbatar da za a kara kudin ba. (NAN)