✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPOB ta kai hari ofishin Hukumar Shige da Fice a Abiya

Bam ya tashi a ofishin Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar.

Kungiyar IPOB ta kai farmaki ofishin Hukumar Shige da Fice ta Kasa da ke Ubakala, a Karamar Hukumar Umuahia ta Kudu a Jihar Abiya.

Harin na zuwa ne awa biyu bayan harin bam da aka kai ofishin Sashen Binciken Manyan Laifuka, wanda ya yi sanadin rasa rayukan mutane da dama.

Ofishin Hukumar Shige da Fice a Jihar da ke kusa da ofishin ’yan sanda na Ubakala an kai masa harin ne a ranar Asabar.

Ofishin ’yan sandan na Ubakala na daga cikin caji ofis din da IPOB ta kai hari a baya-bayan nan, inda ta kashe jami’an ’yan sanda biyu.

Kakakin ’yan sandan Jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna, bai daga waya ba yayin da wakilinmu ya tuntube shi don jin gaskiyar faruwar harin.