✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta sake kai hari Borno

ISWAP ta sake kai hari Borno bayan kwana biyu da kashe Birgediya Janar Dzarma Zirkusu.

Ana zargin mayakan kungiyar ISWAP masu da’awar jihadi a Yammacin Afirka sun sake kai hari Karamar Hukumar Askira Uba da ke Jihar Borno.

Wakilinmu ya ruwaito cewa mayakan sun cinna wa gidaje da dama wuta a kauyen Dille.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun kutsa kauyen ne da misalin karfe 5.30 na yammacin ranar Litinin.

Majiyar ta ce mayakan sun kwashe kayayyaki masu tarin yawa a shaguna musamman kayyayakin abinci, sannan daga bisani suka cinna wa gidajen mazauna kauyen wuta.

Sai dai har ya zuwa lokacin kawo wannan rahoto, babu wani karin bayani dangane da girman ta’asar da maharan suka tafka.

Kwanaki biyu da suka gabata ne mayakan ISWAP suka yi wa garin Askira dirar mikiya da misalin karfe bakwai na safiyar Asabar a cikin jerin gwanon motoci, suna luguden wuta babu kakkautawa.

A yayin harin na kwanton bauna ne mayakan na ISWAP suka harbe wani Birgediya-Janar din soji da kuma wasu sojojin hudu a Bulguma, wani yanki da ke kusa da garin Askira na Karamar Hukumar Askira Uba a Borno.

Aminiya ta ruwaito cewa, mayakan sun kashe Birgediya-Janar Dzarma Zirkusu, wanda tuni Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya jajanta wa iyalansa da sauran sojojin da suka riga mu gidan gaskiya.

Bayanai sun ce sojojin Najeriya sun aika kwamandojin ISWAP 50 lahira a wani harin ramuwar gayya da suka kai wa kungiyar bayan harin da ya yi ajalin Birgediya-Janar Dzarma Zirkusu.

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojojin Bataliya ta 115 ta Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya sun yi wa mayakan kungiyar sammako da luguden wuta ne a yankin kauyen Leho da kewaye a jihar Borno.

Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya ce, “Sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) sun kashe kwamandojin ISWAP akalla 50 tare da lalata makamansu a harin ramuwar gayya da suka kai  wa kungiyar a Karamar Hukumar Askira Uba ta Jihar Borno.

“A harin ne sojoji suka tarwatsa motocin kungiyar masu sulke da wasu motoci 11 da aka girke manyan bindigogi a ciki gami da wasu manyan bindigogi,” masu matukar hari.