✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Italiya da Argentina: Paparoma ya rasa kungiyar kwallon kafar da zai goyi baya

Paparoma Francis ya yi wa ’yan kwallon Argentina da Italiya barkwanci kan wai ya rasa wadanda zai goyi baya a wasannin sada zumunci da suka…

Paproma na karbar kyauta daga Messi na  Argentina da Mai tsaron gida Gianluigi Buffon a fadar VaticanPaparoma Francis ya yi wa ’yan kwallon Argentina da Italiya barkwanci kan wai ya rasa wadanda zai goyi baya a wasannin sada zumunci da suka kara a birnin Rum. “Wannan al’amari zai yi mini wuya, domin akwai sa’a a wasan sada zumunci. To mu tabbatar mun zama daya,” a cewar limanin addini, wanda dan asalin Argentina ne, a lokacin da yake ganawa da Lionel Messi da Mario Balotelli, tare da sauran tawagar ’yan wasan.
Paparoma Francis, tsohon magoyon bayan Kulob din San Lorenzo na argentina ne, don haka ya yi kira ga kungiyoyin kwallon kafar da su yi amfani da shahararsu wajen nuna kyawawan misalai ga magoya bayansu: “Ya ku ’yan wasa abin kaunata, kun shahara. Mutane na koyi da ku, har a wajen filin wasa. Don haka nauyin kyautata ma’amala ya hau kanku,” inji shi.
“A fadar batican , suna fadar cewa ba ni da tarbiyya!” a barkwancin da ya yi dan gaban kulob din AC Milanm Balotelli, wanda kafafen yada labarai ke yawan bada labarin rashin tarbiyyarsa.
 “aikata sabbanin haka kuwa, to zai tabbatar a kwai rauni a cikin kungiyar kwallon, koda kuwa ku n kashe wasa. Ba a la’akari da daidaiklun mutane, ana lura ne kawai da ’ya’yan kungiya baki daya,” a cewarsa.
Shi kuwa tauraron kwallon Argentina Messi, wanda ba zai buga wasan ba, ya tabbatar da cewa, al’amuran da Paparoma ya bijiro da su duk gaskiya ce. “karrama mutane har ma da abokan hamayya, shi ne tushen komai, a filin wasa da sauran harkokin rayuwa,” inji shi.
Ya ce: “Mu ’yan wasa, muna taka rawa wajen isar da sakon Paparoma, ta hanyar buga wasa mai kayatarwa, don gamsar da butarsa,” a cewarsa.
Paparoma ya gargadi kungiyoyin biyu, da su kauce wa duk wani abu da ya shafi tashin hankali da son kudin da za a ci a cikin wasan.