✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jahilar mace masifa ce – Laure Maso Kano

Hajiya Laure Umaru Maso-Kano, tsohuwar malamar makaranta ce kuma ’yar kasuwa a garin Nguru, Jihar Yobe. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da…

Hajiya Laure Umaru Maso-Kano, tsohuwar malamar makaranta ce kuma ’yar kasuwa a garin Nguru, Jihar Yobe. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da wasu harkoki na daban:

Tarihina

Sunana Hajiya Laure Umaru Maso-Kano an haife ni garin Nguru a Jihar Yobe, ranar 1 ga Yulin 1983. Na shiga yi makarantar Firamare a ta Hausari a 1988 na gama a 1993, sannan na tafi makarantar  Sakandare  ta Army Day Secondary School Nguru daga 1993 na kammala a 1999. Ina gama sakandare sai aka yi mini aure, bayan na yi aure ne na tafi na yi difloma a bangaren shari’a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2006. Da na gama a shekara ta 2008 zuwa 2013 na tafi na yi digiri na farko a bangaren Nazarin Addinin Musulunci a Jami’ar Maiduguri yanzu haka ina shirye shiryen tafiya yin digiri na biyu.

Aiki

Na fara aiki ne a lokacin da na gama sakandare inda na fara aikin koyarwa a firamaren Inglewa da ke garin Nguru, a lokacin da na yi aure sai na bar koyarwa na koma Abuja, ina nan ba na aikin komai har sai da na gama digiri dina inda yanzu nake aiki a Hukumar Nazarin Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS) a Jihar Kano.

Kalubale

Gaskiya a yanzu ban fuskanci kowane irin kalubale ba, amma dai na san aikin gwamnati akwai kalubale a cikinsa musamman ga ’ya mace da take aiki a tsakanin maza. Ba kowane namiji ba ne yake son ganin ci gaban mace a wajen aiki.

Nasara

Alhamdulillahi babbar nasarar da na samu a rayuwa ita ce yadda na samu aiki nake yi nake dogaro da kaina ba tare da na zame wa mutane matsala ko na dora musu wata dawainiya ba, kuma insha Allah wannan aiki zai kai ni inda ban yi tsammani ba a rayuwa.

Tufafi

A matsayina ta Bahaushiya kuma ’yar Arewa na fi son in sanya doguwar riga ta atamfa wacce ba ta matse ni ba, inda ko’ina zan iya shiga ba wanda zai ce min na yi shigar da ba ta dace ba, kuma za a yi mini kallon mutunci da kamala.

Abinci

Na fi sha’awar tuwo da miyar ganye ko shinkafa da wake da mai da yaji ko kuma da miya.

Kungiya

Ni mamba ce a kungiyoyi da dama tun ina sakandare har na shiga jami’a, Yanzu haka ina cikin wata kungiya ta Aspire Women Forum ta Jihar Yobe.

Kasashen da na ziyarta

Na je kasar Saudiyya na kuma je Dubai a kasar Daular Larabawa (UAE ) harkar kasuwanci domin ni ’yar kasuwa ce.

Iyali

Alhamdullah ina da ’ya’ya biyar, namiji daya da mata hudu kuma dukkansu suna raye.

Burina a rayuwa

A rayuwata ba ni da wani buri da ya wuce in ga na kafa wata gidauniya ta kashin kaina da zan yi amfani da ita wajen taimakon mata da kananan yara musamman don share musu hawaye a bangarorin rayuwa.

Shawara ga mata

A matsayina ta mace ina amfani da wannan dama in bai wa iyaye shawara mu yi kokari mu tsaya wa yaranmu mata su yi karatun zamani da na addini. Saboda karatun ’ya mace a wani lokaci ya fi na da namiji muhimmanci sosai. Domin duk macen da take da ilimi yanayin rayuwarta daban ne da na wacce ba ta da ilimi.

Sannan idan aka ilimantar da ’ya mace baki daya al’umma aka ilimantar, domin ita uwa makaranta ce ta farko da take fara kula da tarbiyyar ’ya’yanta tun daga gida.

A gaskiya jahilar mace masifa ce, ko a zaman makwabtaka ballanta a ce za ka aure ta ku samu iyali da ita. Saboda haka yana da muhimmaci mu ilimantar da yaranmu mata idan muka yi haka mun taimaki kanmu kuma mun taimaki ita yarinyar da kuma duk wanda zai aure ta.