✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’a sun daka wa motocin abinci wawa a hanyar Abuja

An yi awon gaba buhunan shinkafa da kwalayen taliya da sauran kayan abinci daga motocin

Jama’ar gari sun tare hanya suna tare motocin kayan abinci musamman na kamfanin Dangote suna daka musu wawa a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Alhamis.

Wani ganau, Alhassan Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan daban sun tare motoci da dama da suka dauko kayan abinci daga Abuja zuwa Kaduna a daidai Mahadar Suleja da ke kan hayar.

A cewarsa, mutanen sun wasushe buhunan kayan abinci, musamman shinkafa daga motocin kafin sojoji su kawo dauki.

“Sai dai sojoi suka so suka fara harbi a iska domin tarwatsa bata-garin, amma duk da haka mutane da dama a cikinsu sun yi awon gaba buhunan shinkafa da kwalayen taliya da sauran kayan abinci.

“Ga shi mun ji an ce gobe yan acaba za su yi zanga-zangan da suka shirya yi jiya, amma suka dage,” in ji shi.