✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindiga a hanyar Birnin Gwari

An kwato bindiga kirar AK47 da babura hudu a musayar wutar da aka yi da ’yan bindgiar a safiyar Litinin.

Jami’an tsaro sun tarwatsa gungun wasu ’yan bnidiga da suka kai wa matafiya hari a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Jami’an tsaron sun kwato bindiga kirar AK47 da babura hudu bayan musayar wutar da suka yi da ’yan bindgiar a safiyar ranar Litinin.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce, “A lokacin da ’yan sanda daga Buruku suke zagayen sintiri a yankin Udawa da ke kan Babbar Hanyar Kaduna-Birnin Gwari ne ’yan bindiga suka yi musu kwanton bauna, a kokarinsu na far wa matafiya.

“Nan take ’yan sandan tare da ’yan banga suka bude musu wuta babu kakkautawa, inda ’yan bindigar suka tsere dauke da raunin harbi a jikinsu, suka bar bindigarsu daya kirar AK 47 da kuma baburansu guda hudu.

“An kai kayan da aka kama ofishin ’yan sanda da ke Buruku, an kuma ci gaba da kokarin ganin an kamo bata-garin sun fuskanci hukunci,” inji shi.

A cikin sanarwar, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Yekini A. Ayoku, ya bukaci al’ummar yankin da su kasance masu lura tare da sanar da jami’an tsare game da duk wata barazabar tsaro.