✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Janye murabus din Malami da Ngige ya saba wa doka —Falana

Lauyan ya ce dole a sake tura wa majalisa sunayen ministocin da suka janye murabus dinsu kafin a sake nada su.

Babban lauyan nan mai rajin kare hakkin bil Adama, Femi Falana (SAN) ya bayyana cewa janye takardar murabus da wadasu ministoci da a baya suka shiga takarar siyasa suka yi ya saba wa doka.

Falana ya bayyana haka ne bayan Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Ministan Kwadago, Chris Ngige, sun janye daga tsawa takara a zaben 2023, alhali sun mika takardarsu ta ajiye aiki da farko.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, Falana ya ce “Yin murabus na kowane ma’aikaci daga kowane oifishi kamar yadda yake a cikin Kundin Tsarin Mulki zai soma aiki ne daga lokacin da wasikar yin murabus ta isa ga hukuma ko wanda takardar ke dauke da adireshinsa ko kuma duk wanda hukuma ta amince ya karbi takardar.”

Ya kara da cewa abin da masu rike da mukaman siysa suka yi na ci gaba da zama a kan mukamansu bayan da farko sun mika takardar sauka daga kujerunsu ga Shugaban Kasa, ya saba wa Sashe na 306 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Don haka Falana ya bayyana cewa,  “Idan har za a sake nada ministocin da suka janye wasikarsu ta murabus, Sashe na 147 na Kundin Tsarin Mulki ya bukaci Shugaban Kasa ya sake mika sunayensu ga Majalisar Daddatwa don ta sake tantance su.”

Kafin wannan lokaci, Shuagaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministocinsa da masu rike da mukaman gwamnati da ke burin shiga takara a zaben 2023, su yi murabus daga mukaminsa zuwa ranar 16 ga Mayu.