✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janyewar Amurka: Ina makomar Afghanistan bayan kama mulkin Taliban?

A baya, Taliban ta hana sauraron kade-kade, ta yanke hannuwan barayi ta kuma jefe mazinata

A karshe dai Amurka ta kwashe nata-ya-nata ta bar Afghanistan bayan shekara 20 tun kifar da Gwamnatin Taliban.

A tsawon wannan lokaci, kungiyar ta Taliban ta yi ta fafatawa da gwamnatin kasar mai samun goyon bayan kasashen Yamma, tun daga shekarar 2001.

Kungiyar dai ta bulla ne a shekarar 1994 a matsayin daya daga cikin bangarorin da suka fafata yakin basasar kasar, sannan daga bisani ta karbe iko da mafi yawan sassan kasar a 1996, sannan ta kaddamar da Shari’ar Musulunci.

Abokan adawarta da ma kasashen Yamma da dama sun zarge ta da kakaba wa mutane tsarin Shari’ar Musulunci ba tare da son ransu ba, da kuma musgunawa mabiya wasu addinan marasa rinjaye a kasar.

Wanda ya kirkiri kungiyar, Mullah Mohammad Omar, daga bisani ya tsallake ya bar kasar bayan dakarun gwamnati da suka sami tallafin Amurka sun hambarar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

Taliban dai ta sake kwace mulkin Afghanistan mako biyu gabanin ficewar dakarun Amurka da na kungiyar kawance ta NATO daga kasar.

Kungiyar ta kwace iko da kusan dukkan manyan biranen kasar a cikin ’yan kwanaki kalilan.

Da janyewar Amurka a ranar 31 ga watan Agusta, ana sa ran a ranar Laraba ko kashegari kungiyar za ta kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Abin da yake faruwa a kasar

Taliban dai ta jagoranci Afghanistan a shekarun 1990 zuwa 2001, lokacin da dakarun kasar da gudunmawar Amurka suka taimaka wajen hambarar da gwamnatinsu.

Dakarun kawancen dai, wadanda Amurka ke yi wa jagoranci, sun fatattaki kungiyar daga mulki, ko da yake ba su bar kasar baki daya ba, inda suka sake dawowa don kwace mulkin kasar mako biyu da suka gabata.

To sai dai lamarin ya jefa tsoro a zukatan mutanen kasar wadanda suka rika tururuwa zuwa filin jirgin saman Kabul, babban birnin kasar, da nufin gudun hijira.

Hakan ba zai rasa nasaba da la’akari da yadda kungiyar ta gudanar da mulkinta shekaru 20 da suka gabata ba, da kuma yadda suke fargabar tarihi na iya maimaita kansa.

Amma kungiyar ta ce mulkinta na wannan karon zai bambanta da na baya, kuma za ta tabbatar da kiyaye hakkin dan Adam, ciki har da kare hakkin mata.

Sai dai hakan bai hana mutanen kasar yin dari-dari da su ba.

Dalilin tururuwar barin kasar

Galibin mutane dai na fargabar cewa kungiyar za ta yi ramuwar gayya ne idan ta fara mulki, musamman a kan wadanda suka yake ta ko suka goyi bayan dakarun Amurka a baya.

Kazalika, mutane da dama na fargabar cewa Taliban za ta dawo da nau’in Shari’ar Musuluncin da ta yi a baya, wadda galibinsu ke ganin ta tsaurara.

Mulkin Taliban a baya

A lokacin dai, kungiyar ta haramta wa mata zuwa makaranta ko yin aiki a waje, sannan ta tilasta musu sanya sutura mai rufe jiki baki daya, kuma dole sai wani dan uwansu namiji ya raka su a duk lokacin da za su fita.

Taliban ta kuma hana sauraron kade-kade, ta rika yanke hannuwan barayi da kuma jefe mazinata.

A shekarar 1996, Taliban ta ayyana kasar a matsayin Masarautar Musulunci ta Afghanista.

A gwamnatance dai, kungiyar ta gudanar da mulki daidai da irin tsarin gwamnati na zamani, amma a kan tituna kuwa, sai yadda suka dama haka mutanen kasar suka sha.

Filin jirgin saman Kabul

Dubban ’yan kasar Afghanistan da baki ne suka rika tururuwar guduwa daga kasar saboda fargabar salon mulkin Taliban.

Wasu daga cikinsu sun yi kokarin ficewa ta kowanne hali, ciki har da masu shiga fuka-fukin wani jirgin yakin Amurka, lamarin da daga bisani ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu.

Akalla dai mutum bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar yamutsin, kamar yadda Rundunar Sojin Kasa ta Amurka ta tabbatar.

Me ya sa Taliban ta karbi mulki a yanzu?

Watakila Taliban ta sami nasarar karbar mulki ne sakamakon janyewar da sojojin Amurka suka sanar da yi a karshen watan Agusta.

Tsawon shekaru dai Amurkar ke ta kokarin ficewa daga kasar bayan shafe tsawon lokaci ana gwabza yaki.

Dakarun Amurka dai sun hambarar da gwamnatin Taliban a wancan lokacin ne, ’yan watanni kadan bayan sun mamaye kasar, bayan sun zarge ta da bayar da mafaka ga Al-Qaida wadda aka zarga da kai harin ranar 11 ga watan Satumba na 2001.

Sai dai a bara, tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da shirin kasarsa na janye dakarunta daga Afghanistan bayan cimma wata yarjejeniya da ta takaita yawan kai musu hare-hare.

Daga bisani kuma Shugaba Joe Biden ya sanar da cewa rukunin karshe na dakarun Amurka za su bar kasar a karshen watan Agusta.

Ko da lokacin ya karato ne sai kungiyar ta zafafa da kai hare-hare tana kwace biranen kasar daya bayan daya.

Rushewar dakarun Afghanistan

Galibi dai ana nuna yatsa ga cin hanci da rashawa da ya yi wa Rundunar Sojin Afghanistan katutu da cewa shi ne ummul haba’isin wargejewarta.

Amurka da NATO a tsawon shekaru sun kashe biliyoyin Daloli wajen bayar da horo da kuma samar da kayan aiki ga sojojin kasar, amma rashawa ta yi wa gwamnatin kasar katutu.

An dai zargi kwamandojin rundunar da dama da karkatar da kudaden kasar sannan suka ki samar wa dakarunsu isassun makamai, a wasu lokutan ma hatta abin da za su ci gagarar su yake yi.

Bugu da kari, gwiwarsu ta dada yin sanyi ne lokacin da suka ji cewa Amurka za ta janye daga kasar.

Ko da Taliban ta kara kaimi wajen ganin ta kwace iko, sojoji da dama sun rika mika wuya cikin ruwan sanyi, yayin da kungiyar ta kama birane da dama ciki har da Kabul ba tare da samun wata turjiya ba.

Shugaban Afghanistan

Ya cika wandonsa da iska.

Shugaba  Ashraf Ghani dai ya yi batan dabo kuma a ’yan lokuta kadan ne aka ji duriyarsa tun lokacin da Taliban ta zafafa da kai hare-hare a kasar.

Daga bisani bayan sun shiga Kabul sai ya cika wandonsa da iska, inda ya ce ya yi hakan ne don kauce wa zubar da jini.

Me zai faru nan gaba a Afghanistan?

Babu wanda ya san me zai iya faruwa a nan gaba idan Taliban ta fara mulki.

Kungiyar dai ta ce tana son kafa gwamnatin Musulunci wacce za ta tafi da kowa da kowa ba tare da bangaranci ba.

Tuni dai tattaunawarsu ta yi nisa da manyan ’yan siyasar kasar, ciki har da wasu jagororin tsohuwar gwamnatin kasar.

Sun dai yi alkawarin kafa Shari’ar Musulunci tare da kiran mata da su shigo a dama da su a gwamnati, suna masu alkawarin dawo da rayuwar da aka saba a baya kafin fara yaki.

Sai dai ’yan kasar da dama na fargabar cewa za su fuskanci musgunawa daga mulkin kungiyar.

Kazalika, suna kuma fargabar cewa za a samu rashin doka da oda a kasar bayan an saki dubban fursunoni daga gidan yari, sannan jami’an tsaro na guduwa.

Ko Taliban za ta sake ba Al-Qaida mafaka?

Kungiyar dai ta yi alkawarin cewa ba za a sake amfani da ita a matsayin mafaka ba wajen kai wa kasashe hari, kamar yadda yake kunshe a cikin wata yarjejeniya da suka kulla a 2020.

To sai dai duk da haka sojojin Amurka sun ce suna dari-dari.

Ko a watan da ya gabata, wani babban jami’i a Ma’ailayar Tsaron Amurka ta Pentagon ya ce kungiyoyi masu tsauttsauran ra’ayi irin na Al-Qaida  za su iya sake bulla a kasar kuma su ci gaba da kara karfi fiye da kowanne lokaci a baya.

Kungiyar Taliban dai ta fuskanci mummunan sakamako saboda irin rawar da ta taka a harin ranar 11 ga watan Satumban 2001, kuma tana fatan ganin ta kauce wa ganin tarihi ya maimaita kansa a lokacin mulkinta.

Babban abin jira a gani dai a yanzu bai wuce yaya kamun ludayin kungiyar zai kasance bayan ta kama mulkin kasar ba, kuma ko za ta cika alkawuran da ta dauka, kuma za ta koma salon mulkinta na baya.

Lokaci ne kawai zai tantance hakan!