✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jaruman fim da suka kwanta dama kwanan nan

Masana'antun biyu sun yi rashin jiga-jigan jarumansu a baya-bayan nan.

Masana’antun Shirya Fina-finai na Kudancin Najeriya Nollywood da na Hausa Kannywood, sun yi rashin jiga-jigan jarumansu a ’yan kwankin nan.

Da dama daga cikin jaruman da suka riga mu gidan gaskiya sun jima suna jan zarensu a masana’antar.

Daga cikin waɗanda mutuwarsu ta girgiza ’yan Najeriya a Kannywood akwai Darakta Amini S. Bono da Usman Baba Pategi (Samanja) sai kuma ta ƙarshe Saratu Gidado (Daso).

A Nollywood ta Kudancin Najeriya, akwai irin su Tolani Quadri Oyebamiji da ake kira da Sisi Qadr da Ethel Ekpe da kuma Cif Adedeji Aderemi da aka fi sani da Olofa.

A cikin waɗanda suka mutu daga Nollywood akwai John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu da kuma Amaechi Muonagor.

Waɗanda har yanzu ake alhinin mutuwarsu akwai Saratu Gidado (Daso) wadda ta mutu ranar Talata 9 ga watan Afrilu, 2024.

Saratu Gidado (Daso)

An haifi Daso a ranar 17 ga watan Janairu, 1968 a birnin Kano, ta rasu tana da shekara 56 a duniya.
’Yan uwan Daso, sun bayyana wa manema labarai cewa, ta rasu ne bayan ta koma barci bayan sahur.
Ta fara shahara  a 2000 a wani fim mai suna ‘Linzami Da Wuta’, wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya.
Daga cikin fina-finan da suka haska tauraron Daso akwai Nagari, Gidauniya, Mashi, da kuma Sansani.
Darakta, Aminu S. Bono
Aminu S. Bono
An haifi Aminu Suraj Bono a ƙwaryar birnin Kano.
Ya fara fitowa a masana’antar fina-finan Kannywood a cikin fim ɗin Agola a shekarar 2017.
Aminu, ya rasu ranar Litinin da yamma a watan Nuwamba, 2023
Bono, ya fito a cikin fina-finan Kannywood da dama,  an shafe sama da shekara 20 damawa da shi a masana’antar.
 Usman Baba (Samanja)
Samanja Usman Baba Fategi

Jarumi Usman Baba wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama ya rasu yana da shekara 84 a duniya. Ya bar mata biyu da ‘ya’ya 12.

Ya rasu a watan Nuwamba a 2023.
Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka jima ana yi da shi a fagen wasannin kwaikwayo kafin zamani ya bar shi a baya.
Masa’antar fina-finai ta Kudancin Najeriya, ta rasa jarumai da dama.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai:
Mista Ibu
John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu ɗan wasan kwaikwayo ne, ya shahara wurin iya magana da ban dariya kwarai da gaske.
Mista Ibu  mutu a ranar 2 ga watan Maris, 2024.
Mista Ibu ya rasu ne a wani asibiti a Jihar Legas, ya rasu  yana da shekara 62 a duniya.
An haifi Mista Ibu ne a ranar 17 ga wata Oktoba, 1961 a Jihar Enugu.
Amaechi Muonagor
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Amaechi Muonagor, ya rasu yana da shekara 62 a duniya bayan doguwar jinya.
Ya yi fama da jinya kafin daga ƙarshe ya mutu ranar 24 ga watan Maris, 2024 sakamakon ciwon ƙoda.
Ya rasu kwanaki kaɗan bayan bayyanar wani faifan bidiyonsa, inda ya nemi a taimaka masa a yi masa dashen ƙoda.
Muonagor, ya fito a fina-finan Nollywood da dama.
Ethel Ekpe
Tsohuwar jaruma Ethel Ekpe, ta rasu ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024 a Jihar Legas.
Ta rasu ne bayan ta yi fama da cutar daji.
Ta taka rawar gani a shirin ‘Segi’, shirin gidan talabijin na NTA
Sisi Qadri
A watan Maris din 2024 ne, aka sanar da rasuwar fitaccen ɗan wasan barkwanci na harshen Yarbanci, Tolani Quadri Oyebamiji, wanda aka fi sani da Sisi Quadri.
Ya rasu yana da shekara 44 a duniya.
Masana’antun biyu sun yi rashin jiga-jigan jarumansu a baya-bayan nan, lamarin da bar da yawa daga cikin masana’antun cikin jimami da kaɗuwa.