✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin wayoyi 43 da WhatsApp zai daina aiki a kansu daga watan Nuwamba

A duk shekara, kamfanin kan dakatar da wasu wayoyi daga amfani da manhajarsu.

Daga watan Nuwamban 2021, manhajar nan ta aikewa da sakonni a shafin sada zumunta wato WhatsApp za ta daina aiki a wasu manyan wayoyi har guda 43.

A cewar kamfanin, kamar yadda jaridar India Times ta wallafa, wayoyin da lamarin zai shafa hada da masu amfani da manhajar Android 4.1 da Apple iOS 10 da kuma Kai OS 2.5.1.

Sai dai hakan ba wai yana nufin idan wayarka na cikin jerin manhajar za ta daina aiki nan take ba ne, akwai yuwuwar ka iya ci gaba da amfani da ita matukar kamfanin wayarka zai baka damar daga darajarta (upgrade).

Manhajar dai na taka muhimmiyar rawa a harkokin aikewa da kuma karbar sakonni a duniya, inda alkaluma suka nuna sama da mutum biliyan biyu ne ke amfani da ita.

Sai dai a kowacce shekara, kamfanin kan dakatar da wasu nau’in wayoyi daga ci gaba da amfani da manhajarsu.

A bana ma, kamfanin ya wallafa jerin wayoyin da zai daina aiki a kansu.

Idan kana son sanin wayoyin da sauyin zai shafa, kamfanin na WhatsApp ya bayyana jerin sunayensu.

Apple iPhone

iPhone SE da iPhone 6s da kuma iPhone 6s Plus, matukar ba a daga manhajarsu zuwa IOS 10 ba.

Ko da yake, za a iya daga manhajar iPhone SE, 6s da 6s Plus zuwa iOS 14, wanda zai ba masu amfani da sudamar ci gaba da amfani da manhajar.

LG

LG Lucid 2 da Optimus F7 da Optimus F5 da Optimus L3 II mai layi biyu da Optimus F5 da Optimus L3 II da Optimus L4 II da Optimus L4 II mai layi biyu da Optimus L5 da Optimus L5 II da Optimus L5 mai layi biyu da Optimus L7 da Optimus L7 II mai layi biyu da kuma Optimus L7 II.

Sauran sun hada da Optimus F6 da Enact da Optimus F3 da Optimus L2 II da Optimus Nitro HD da Optimus 4X HD da kuma Optimus F3Q.

ZTE

A bangaren wayoyin kamfanin ZTE kuwa, jerin wayoyin da lamarin zai shafa sun hada da ZTE Grand S Flex da ZTE Grand X Quad V987 da ZTE Grand Memo da kuma ZTE V956.

Huawei

Wayoyin Huawei Ascend Mate da Huawei Ascend G740 da Ascend D Quad XL da Ascend D1 Quad XL da Ascend P1 S da Ascend D2 sune wadanda kamfanin ya ce sauyin zai shafa.

Sony

Akwai nau’in wayoyi guda uku na kamfanin Sony da lamarin zai shafa wadanda suka hada da Sony Xperia Miro da Sony Xperia Neo L da kuma Xperia Arc S.

Samsung

Wayoyin kamfanin Samsung kuma da sauyin zai shafa sun hada da Samsung Galaxy S2 da Galaxy S3 mini da Galaxy Trend Lite da Galaxy Trend II da Galaxy Core da Galaxy Ace 2 da kuma Galaxy Xcover 2.

Sauran kamfanoni

Sauran kamfanonin wayar da za su daina aiki da manhajar daga watan na Nuwamba sun hada da Wiko Darknight da Alcatel One Touch Evo 7 da Archos 53 Platinum da Caterpillar Cat B15 da Wiko Cink Five da Lenovo A820 da UMi X2 da Faea F1 da THL W8 da kuma wayar HTC Desire 500.

Daga: India Times