✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasa ya yi hatsari a Legas

Jirgin kasan ya taho a sukwane ya yi karo da wata mota da safiyar Litinin

Jirgin kasa a sukwane ya yi karo da wata mota kirar Volkswagen a unguwar Oshodi a Jihar Legas.

Hatsarin ya faru a safiyar Litinin da misalin large 8:15, ko da yake babu cikakken bayani kan musabbabin abun da ya faru amma dai motar na kan layin dogo ne sadda abun ya faru.

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta watsa hotunan faruwar lamarin a lokacin da ta je inda hatsarin ya faru.

“Wani jirgin kasa ya yi karo da wata mota kirar Volkswagen T4 a magamar ARENA, inda ya tura ta gadar Oshodi U-bridge.

“Masu kallon abun da ya faru sun kara dagula lamarin. Masu kai dauki na hukumar da ke da alhakin dauki sun isa wuri”, kamar yadda aka bayyana a shafinta LASTMA na tiwita