✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin ruwan Sudan ya nitse da tumaki 15,000 a hanyarsa ta zuwa Saudiyya

Jirgin dai na kan hanyarsa ce ta zuwa Saudiyya

Wani jirgin ruwa da aka yi wa lodi fiye da kima ya nitse da tumaki sama da 15,000 a tashar tekun Red Sea da ke kasar Sudan a ranar Lahadi, ko da yake ilahirin ma’aikatan jirgin sun tsira.

Jirgin dai ya nitse ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya daga Sudan, bayan da aka yi ittifakin an lafta masa kaya fiye da yadda ya kamata ya dauka.

Wani babban jami’in tashar jiragen ruwa ta Sudan, ya ce, “Jirgin ruwan, mai suna Badr 1, ya nitse ne da sanyin safiyar Lahadi. Yana dauke ne da tumaki 15,800, adadin da ya haura abin da ya kamata ya dauka.

Jami’in ya ce a ka’ida, tumaki 9,000 ya kamata jirgin ya dauka.

Shi ma wani jami’in wanda ya tabbatar cewa an ceto dukkan ma’aikatan jirgin, ya nuna damuwa kan illar da hatsarin zai jawo wa tattalin arziki da muhalli.

Ya ce, “Nitsewar jirgin za ta shafi hada-hadar tashar jiragen ruwan. Za kuma ta kawo barazana ga muhalli la’akari da yawan dabbobin da suka mutu a cikin jirgin a lokaci guda.

Shugaban Kungiyar Masu Fitar da Kaya zuwa wajen kasar, Omar Al-Kalifa sai da jirgin ya dauki tsawon awoyi yana tangal-tangal kafin ya kife, lamarin da ya ce za a iya ceto shi kafin faruwar iftila’in.

Darajar dabbobin da suka nitse dai ta kai Dalar Amurka miliyan hudu, kamar yadda Saleh Salim, Shugaban Dillalan Dabbobi na kasar ya tabbatar.

Ya ce tumaki kusan 700 ne kacal aka iya cetowa daga jirgin, kuma su ma sun jigata sosai, ba lallai ne su yi tsawon rai ba.

Ya kuma yi kira da a gudanar da zuzzurfan bincike don gano musabbabin hatsarin.