✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin sama dauke da mutum 132 ya yi hatsari a China

Kawo yanzu babu bayanin adadin mutanen da hatsarin jirgin ya yi ajainsu

Wani jirgin sama dauke da fasinja akalla 132 ya yi hatsari a yankin Guangxi  da ke Kudu maso Yammacin kasar China.

Gidan talabijin na gwamnatin China (CCTV) ya ambato Hukumar Agajin Gaggawa ta kasar an cewa an ga tsahin tartsatsin wuta a wani tsauni bayan faduwar jirgin a safiyar Litinin a kusa da kauyen Wuzhou.

“Jirgin kamfanin China Eastern Airlines kirar Boeing 737 mai dauke da mutum 132 people ya yi rikito a yankin Teng da ke Wuzhou a yankin Guangxi, lamarin da ya haddasa tashin wuta a tsaunin,” a cewar rahoton CCTV.

Kawo yanzu dai babu bayanin adadin mutanen da hatsarin jirgin ya yi ajainsu, amma hukumar ta ce tuni aka tura ma’aikata domin aiki ceto bayan faduwar jirgin kirar Boeing 737.

Kafofin yada labaran kasar sun ce jirgin mai lamba MU5735 bai isa yankin Guangzhou da ya kama hanya ba, bayan tashinsa daga birnin Kunming jim da misalin karfe 5 na asuba, agogon GMT (1:00 na rana agogon China).

Kawo yanzu dai kamfanin jiragen na China Eastern bai fitar wa wata sanarwa ba game da lamarin.