✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juyin mulki: Bankin Duniya ya dakatar da tallafin da yake ba Sudan

Bankin ya ce ya dakatar da tallafin bayan hambarar da gwamnatin da sojoji suka yi.

Bankin Duniya ya sanar da dakatar da tallafin da ya ke ba Kasar Sudan, biyo bayan juyin mulki da sojojin kasar suka yi a ranar Litinin.

Shugaban bankin, David Malpass, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya bayyana damuwar bankin kan yadda abubuwa suka tabarbare a baya-bayan nan a kasar.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da sojoji a Sudan suka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Khartoum, babban birnin kasar, har zuwa ranar 30 ga watan Oktoban 2021.

Janar Ibrahim Adlan, wanda shi ne ke rike da ikon kula zirga-zirgar jiragen saman kasar, shi ne ya sanar da dakatar da tashin jiragen.

Hakan dai na zuwa ne yayin da Sojojin ke ci gaba da Fuskantar matsin lamba daga hukumomin duniya har ma da Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar su saki Fira Minista Abdallah Hamdok da suke tsare da shi.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran ne, bayan da kwamitin tsaronta ya gudanar da taron gaggawa kan halin da kasar ke ciki, bayan juyin mulki da kuma tashin hankali gami da zanga-zangar da dubban mutane ke gudanarwa a kasar.

A jawabin da Sakatare Janar na majalisar, Antonio Guterres, ya gabatar, ya bukaci sojojin da su gaggauta sakin Abdallah Hamdok da Ministocin da suka yi aiki karkashin gwamnatin hadakar kasar.

Sai dai Janar Abdelfatah Al-Burhan, wanda ya jagorancin kifar da gwamnatin, ya mayar wa da majalisar martani, inda ya ce Abdallah Hamdok na tsare ne a gidansa kuma yana cikin koshin lafiya.

Tuni mutane suka rabu kashi biyu a kasar, inda wani bangaren ke goyon bayan kifar da gwamnati da sojoji suka yi.

A daya hannun kuma, wasu na Allah-wadai tare da kira ga sojojin su mayar da mulki ga farar hula, duba da halin kuncin da kasar ke ciki na hauhawar farashin kayayyaki.