An kara farashin man fetur zuwa N151.56 a Najeriya | Aminiya

An kara farashin man fetur zuwa N151.56 a Najeriya

    Ishaq Isma'il

Gwamnatin Tarayya ta kara farashin man fetur zuwa Naira 151.56 duk lita kamar yadda Hukumar kayyade farashin man fetur a kasar PPMC ta sanar.

Hakan na kunshe cikin sanarwar da shugaban hukumar shiyyar Ibadan, D.O Abalaka ya fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2020.

Yana cewa: “Ku sani cewa mun sanya sabon farashin sayar da man fetur kuma a yanzu farashin sa zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida duk lita.”

“Wannan sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 2 ga Satumban 2020,”inji shi.