✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kanawa sun gano sabuwar fasahar adana albasa don kasuwancinta

Sabuwar fasahar za ta rage yawan asarar da manoman albasar ke tafkawa

Tsawon shekaru manoman albasa suna tafka asara saboda rashin nagartattun hanyoyin adanata, bayan cire ta.

Wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa, kusan kaso 60 cikin 100 na albasar da ake nomawa takan lalace saboda rashin fasahar adanata.

Manoman Jihar Kano kamar takwarorinsu na sauran jihohin kasar nan suna daga cikin wadanda suke fama da wannan matsala ta lalacewar albasar tare da tafka asararta.

Malam Sanusi Maitaki shi ne Shugaban kungiyar Manoma da Masu Sarrafa Albasa ta kasa (NOPPMAN), reshen Kasuwar Badume da ke karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano, kuma a cewarsa, manoman yankin sun shafe tsawon shekaru suna neman mafita daga wannan matsala da ke kako cikas ga harkarsu.

Ya ce, manoman yankin na noma albasa mai dimbin yawa, amma karancin hanyoyin adanata don ta dade da kuma irin asarar da hakan ke jawo musu suka sa wasu daga cikinsu suka fara tunanin komawa noman wasu kayan amfanin gona maimakon albasar.

Malam Sunusi ya ce, “Ko shakka babu,, a tsawon shekaru albasa na daya daga cikin amfanin gona da ke kawo wa manoma alheri mai yawa, amma hanyar da za su adanata ce babbar matsalar da suke fuskanta.

“Amma cikin ikon Allah, wannan a yanzu ta ta sam ma zama tarihi saboda sabuwar fasahar da shirin Sasakawa (SAA) ya kawo mana, a karkashin Hukumar Bunkasa Noma da Kiwo ta Jihar Kano (KSADP), wadda za ta rage asarar da muke tafkawa,” inji shi.

Shi ma a nasa bangaren Babban Jami’in Bunkasa Kasuwanci na Sasakawa, Mista Isaac Eni, a yayin rangadin kafafen yada labarai na 2022 ya ce za a kafa sabuwar fasaha a karkashin Hukumar KSADP, wadda Bankin Musulunci ya dauki nauyi ta hanyar bayar da bashi da kuma wani tallafi daga Asusun LLF, wanda Sasakawa ke gudanarwa a karkashin kular Hukumar Bunkasa Aikin Gona da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) don bunkasa noma da kiwo a jihar.

Ma’ajin NOPPMAN na kasa, Alhaji Isa Magaji ya ce, sun fahimci muhimmanci da tasirin wannan sabuwar fasaha, kuma a shirye suke su yada ta a dukkan yankunan da suka shahara a noman albasa a Najeriya.

“Muna so a kara yawan wadannan cibiyoyin adana albasa, kuma a namu bangaren, za mu ci gaba da fadi-tashin ganin mun karkafa wadannan cibiyoyi a wannan kasuwa da wasu wuraren, saboda gaskiya muna bukatarsu,” inji Ma’ajin.

Babban Jami’in KSADP a Sasakawa, Alhaji Abdulrasheed Hamisu kofar Mata ya ce, a shekarar da ta gabata, an yi kokari matuka wajen fito da sababbin hanyoyin inganta amfanin gona lokacin girbinsa da kuma bayan bayan girbin.

Wasu daga cikin wadannan fasahohi a cewarsa sun hada da kirkiro injinan shuka guda 140 da na dashen shinkafa guda 97 da injinan ban-ruwa guda 244 da injin cire tsakuwa daga shinkafa guda 15 da na turara shinkafar guda 190 da na sheke masara guda 15 da na zuba takin zamani guda 201 da kuma kwandunan zuba tumatir na zamani da sauransu.