✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: ALGON ta gargadi kwamitin Abba kan zafafa siyasa

Kwamitin karbar mulkin yana zargin shugabannin kananan hukumomin kan yin almubazarranci da dukiyar gwamnati.

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen Jihar Kano ta bukaci Kwamitin Karbar Mulki na Jam’iyyar NNPP na jihar da ya daina zafafa siyasa da haifar da tashin hankali ko furta lafuzan da ka iya haifar da hargitsi.

Shugaban ALGON na jihar, Bappa Muhammad ya yi kiran ne a sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kan zargin karkatar da kudaden al’umma da kwamitin ke yi wa shugabannin kananan hukumomin jihar domin bayar da tallafin karashen zaben da ke tafe nan gaba.

Aminiya ta ruwaito shugaban kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi yana gargadin shugabannin kananan hukumomin kan yin almubazarranci da dukiyar gwamnati.

Amma a martaninta kungiyar ta yi kira gare shi da ya yi aiki da hankali domin irin wannan tashin hankalin jama’a ba zai iya tasowa ba a wannan tafiyar ta dimokuradiyya.

“An saba yin irin wadannan zarge-zargen a duk lokacin da aka samu sauyin a shugabanci.

“Muna so musamman mu tunatar da mai yin wadannan zarge-zarge game irin hakan da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2014 na yin amfani da kudaden al’umma da ya karbo daga kananan hukumomi 44 da aka yi wa shugaban kasa buri.

“Idan dai za a iya tunawa dai an yi zargin an karbo makudan kudade har Naira miliyan saba’in daga kowacce daga cikin kananan hukumomi 44 da ke jihar ba bisa ka’ida ba, wanda har yanzu shari’ar tana gaban hukumomi, ta ki da cin hanci da rashawa’’.