✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars ta dakatar da Koci Abdu Maikaba

Dakatarwar ya biyo bayan kafa wani kwamiti wanda zai binciki aikin kociyan tare da ba da shawarar ɗaukar mataki

Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon ƙafa ta Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ’yan wasanta, Abdu Maikaba nan take.

Hakan ya biyo bayan kafa wani kwamiti wanda zai binciki aikin kociyan tare da ba da shawarar daukar mataki na gaba.

Idan dai za a iya tunawa Abdu Maikaba ya yi wasu kalamai na rashin jin dadi daɗi a kwanakin baya game da gudanarwar kungiyar yayin wani taro da magoya bayan Ƙungiyar Kano Pillars suka shirya a cibiyar manema labarai da ke Kano.

Matakin dakatar da shi ya zo ne kwanaki bayan da tsohon dan wasan Enugu Rangers din ya  bayyana cewa bai samu ingantaccen yanayin aiki ba tun lokacin da ya karbi ragamar shugabanci a farkon kakar bana.

“Ina buƙatan yanayi mai kyau don yin aiki; halin da ake ciki yanzu ba shi da kyau a Kano.

“Ina tattaunawa da hukumar gudanarwa a cikin kwanakin nan. Idan har ta ba da izinin dakatar da kwangilar, zan yi hakan,” in ji Maikaba.