✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano ta Tsakiya: Laila Buhari ce ’yar takarar sanatan PDP

Karo na shida ke nan da ta fito neman kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya

Fitacciyar ’yar siyasa a Kano, Laila Buhari, ta lashe zaben fitar da dan takarar Sanata mai wakilatar mazabar Kano ta Tsakiya a jam’iyyar PDP.

Laila Buhari ta samu wannan nasara ne a karo na shida ke nan da Laila Buhari take neman takarar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya, ba tare da ta kai labari ba.

“Wannan abu ne da muka dade muna nema amma hakarmu ba ta cim ma ruwa ba, sai yanzu.

“Ina godiya ga duk wadanda suka shiga aka dama da su musamman maboboin jam’iyyar PDP da suka tabbatar an yi abin da ya dace.

“Wannan babbar nasara ce, musamman ga matasa da mata,” kamar yadda Laila, wadda ta fara siyasa tun a 1981 ta bayyana.

A wannan karon, ta samu kuri’a 323 inda ta kayar da abokin karawarta, Danburam Abubakar Nuhu wanda ya samu kuri’a uku, sai kuma kuri’a biyar da suka lalace.

Laila Buhari ta samu tikitin takarar ne a zaben fitar da ’yan takara da bangaren Sanata Bello Hayatu Gwarzo na PDP ya gudanar.

Zuwa yanzu, fitacciyar ’yar siyasar ta nemi takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a jam’iyyun NPN, UNCP, PDP, PSP, ACN da kuma APC.