✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansilan Kaduna ya nada mashawarta 32 

Ya ce zai fara biyansu da zarar ya rantsar da su

Kasilan mazabar Saminaka da ke karamar hukumar Lere a Jihar Kaduna, Sadiq Abubakar, ya nada wasu matasa su 32 a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Kansilan, wanda ya tabbatar wa Aminiya nade-nafen ya kuma ce za su taimaka masa ne a kan ayyuka daban-daban.

Kansilan wanda kuma shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar karamar hukumar ta Lere, kuma Shugaban Kungiyar Kansilolin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, ya ce a ’yan kwanakin nan, ya nada mutanen.

Ya ce ya yi hakan ne saboda ganin irin gudunmawar da suka ba shi har ya sami kujerar da kuma cancantarsu.

Ya kuma ce ya yi hakan ne domin ya kafa tarihi a siyasar Najeriya.

“Dukkansu babu wanda ya san zan ba shi wannan mukami. Kuma dukkansu matasa ne. Kuma kowa yana da sana’ar yi, kuma akwai mata guda hudu a cikinsu.

“A ranar da zan rantsar da su zan fara biyansu. Saboda mutanen duniya su gane wa idonsu. Kuma nan ba da dadewa ba zan rantsar da su,” inji shi.

Kansilan ya ce wasu na raina kujerar kansila, inda shi a yana ganinta a matsayin babbar kujera ce.

“Don haka duk wanda aka zaba kan wannan kujera, zai iya yin wani abu na taimaka wa al’ummarsa,” inji Kansilan.

Ya ce hakan ne ma ya sa yake fadi-tashin ganin ya kyautata wa al’ummar mazabarsa ta Saminaka.

“Tun kafin na hau kan wannan kujera, na koya wa mata sama da 120 sana’o’i daban-daban a wannan mazaba. Kuma na gyara wani kwalbati a makarantar babbar firamare da ke garin Saminaka.

“Kuma na tara almajirai guda 200 na raba masu takalma. Kuma bayan da na hau kan wannan kujera, na yi abubuwa da dama na taimakawa al’ummar wannan mazaba, don haka ina kira ga kansilolin Najeriya, da mu jajirce mu rika yi wa mutanenmu abubuwan da suke buqata,” Kansila Sadiq.