✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansilolin PDP sun sauya sheka zuwa APC a Kaduna

Kansiloli da wasu jagororin Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar APC mai mulkin jihar.

Kansilolin da aka zaba a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP a Kaduna sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Kansilolin tare da wasu jagororin PDP sun sauya sheka ne kimanin mako guda da tsohon gwamnan jihar, Mukhtar Ramalan Yaro ya fice daga jam’iyyar, ko da yake ba sauya sheka ya yi ba.

Da yake jawabi a madadin kansilolin da suka sauya shekar, kansilan Gundumar Yelwa da ke Karamar Hukumar Chikun, Ishaku Ishaya Dichi, ya ce sun dauki matakin ne saboda gamsuwarsu da kamun ludayin gwamnatin Gwamna Uba Sani.

Honorabul Ishaku Dichi ya bayyana gamsuwarsu da tsare-tsaren da Gwamna Uba Sani ya bullo da su, da ya ce sun inganta rayuwar al’ummar Kaduna.

Ya bayyana cewa rage kudin makaranta, da bayar da tallafin wata-wata ga mabukata da kuma daukar matasa aiki a hukumar tsaron jihar ta KADVIS sun kawo wa al’mmar jihar sauki.

Honorabul Ishaku ya bukaci dan takarar gwamnan jihar na PDP a zaben 2023, Isha Muhammad Ashiru ya janye kararsa ta kalubalantar nasarar Uba Sani a kotu, ya mara masa baya domin ci gaban jihar.

Wani shugaban al’umma, Domicin Aso-Oge ay ce ya sauya sheka ne saboda watsi da shi da aka yi a PDP duk kuwa da sadaukar da kai da ya yi wajen yi mata yakin zabe da sauran hidimomi.

Da yake musu jawabi, Sakataren Tsare-tsaren PDP, Kawu Ibrahim Yakasai, ya yaba musu tare da ba su tabbacin tafiya tare da su a duk harkokin APC domin ci gaban jihar da kuma jam’iyya.