✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanu Nwankwo ya zama shugaban Enyimba

Tsohon ɗan wasan  Super Eagles ta Najeriya da Arsenal ta Ingila, Kanu Nwankwo ya zama shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba dake Aba. Gwamnan jihar…

Tsohon ɗan wasan  Super Eagles ta Najeriya da Arsenal ta Ingila, Kanu Nwankwo ya zama shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba dake Aba.

Gwamnan jihar Abia Alex Otti ne ya naɗa shi wannan shugabanci kamar yadda kakakinsa Kazie Uko ya sanar.

Kanu ya maye gurbin  Felix Anyansi-Agwu wanda ya shugabanci ƙungiyar tsawon shekaru 24.

Ban ji dadin yadda gwamnati ke yunkurin kwace mini Otel ba – Nwanko Kanu

Kanu ya shawarci Ighalo ya ci gaba da yi wa Eagles kwallo

A zamanin Anyansi-Agwu, Enyimba ta ɗauki kofin zakarun Afirka har sau biyu da kuma kofin gasar firimiyar Najeriya sau tara.

A yanzu haka dai, tsohon takwaran Kanu a Super Eagles da Ajax ta Amsterdam, Finidi George ne kocin ƙunigyar.

Kuma shi ya jagoranci Enyimba ta samu nasarar cin kofin ƙwallon ƙafa na Najeriya a karo na tara tare da samun gurbin shiga gasar  ƙofin nahiyar Afirka a baɗi.