✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karfe 9.20 Rasha da Ukraine za su hau teburin sulhu

Rasha da Ukraine za su hau teburin sasantawa a safiyar Litinin a yayin da sojojin Rasha ke dab da shiga Kyiv, babban birnin Ukraine, gami…

Rasha da Ukraine za su hau teburin sasantawa a safiyar Litinin a yayin da sojojin Rasha ke dab da shiga Kyiv, babban birnin Ukraine, gami da ci gaba da luguden wuta a Mariupol, inda hukumomin Ukraine suka ce  an kashe akalla mutum 2,200. 
Zaman sulhun da zai gudana ta bidiyo a tsakanin bangarorin yana zuwa ne a yayin da Rasha ta shafe kusan kwana 20 nata ragargazar makwabciyar tata.
Mai shiga tsakani a bangaren Ukraine, David Arakhamia, ya ce tattaunawar zata fara ne da misalin karfe 8.20 na safiya agogon GMT (9.20 agogon Najeriya), kamar yadda bangarorin biyu suka tabbatar.
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymir Zelensky, ya sanar a safiyar Litinin cewa, “Manufarmu a wannan tattaunawar, a yayin da muke cikin wannan mawuyacin hali, shi ne ganin Ukraine ta samu biyan bukata… zaman lafiya da tsaro.”
Zelensky ya kara da cewa manufar ita ce, “Yin duk abin da ya kamata na tabbatar da ganawar shugabannin kasashen biyu, wanda na tabbata shi ne abin da mutane suke son ganin an yi.”
Wani babban jami’in gwamnatin sulhu daga bangaren Rasha, Leonid Slutsky, ya ce, “Ana samun cigaba tattaunawar,” kamar yadda ya bayyana wa gidan talabijin din gwamnatin Rasha,  RT, ranar Lahadi.

Ci gaba da luguden wuta

Kawo yanzu dai tattaunawar bangarorin ba ta kai ga rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu ba. Da alama kuma Rasha ba za ta saurara ba.
A wani kazamin hari da jiragen yakin Rasha suka kai kusa da kasar Poland, mamba a kungiyar tsaro ta NATO, an kashe mutum 35 tare da jikkata wasu akalla 130 a wani sansanin bada horo na sojojin Ukraine.
A safiyar Litinin Zelensky ya jaddada kiransa ga kungiyar NATO da ta haramta shawagin jirage a birnin Lviv da ake Yammacin kasasa.
“Idan ba ku hana shawagin jirage ba, ba za a dade ba ku ma makamai masu linzamin Rasha za su fada a kasashenku na NATO, a kan ’yan kasashen naku,” inji Zelensky a wani sako ranar Litinin.
Amurka da kawayenta na Tarayyar Turai (EU) sun tura wa Ukraine da tallafin makamai da kudade, suka kuma kakaba wa Rasha takunkuman karya tattalin arziki da ba a taba ganin irinsu ba.
Amma Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, ya ce da wuya kasashen su shiga yakin kai-tsaye, ya kuma gargadi kasashen NATO da cewa yakinsu da Rasha na iya haifar da Yakin Duniya na Uku.
A tattaunawarsu da Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, Mista Biden da shi sun, “jaddada aniyarsu ta kama Rasha da alhakin duk abin da ta aika tare da taimaka wa gwamnati da al’ummar kasar Ukraine,” inji sanarwar da Fadar White House ta Amurka ta fitar.