✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin albashi: Malaman jami’a 48,000 sun tsunduma yajin aiki a Amurka

Suna so a kara mafi karancin albashin zuwa Dala 54,000 a shekara

Sama da malaman Jami’ar Kalifoniya da ke Amurka 48,000 sun tsunduma yajin aiki kan abin da suka kira karancin albashi da rashin yanayin aiki mai kyau.

Malaman dai sun tsunduma yajin aikin ne ranar Litinin a kan abin da suka kira yajin aiki a jami’a mafi girma a tarihin Amurka.

Ana sa ran yajin aikin ya tsayar da harkokin koyo da koyarwa a jami’ar da take da rassa har guda 10 da kuma dalibai sama da 280,000.

Wani dalibin makarantar da ke Sashen Nazarin Tarihi na jami’ar da ke Santa Barbara mai suna Janna Haider, ya ce, “Yanayin da muke ciki ya tabarbare matuka, kuma hakurin mutane da dama a jami’ar nan ya kare.”

Ya kuma ce kimanin kaso 98 cikin 100 na ma’aikatan jami’ar sun goyi bayan shiga yajin aikin a farkon watan Nuwamba.

Yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar rikicin kwadago a Amurka, yayin da ma’aikata ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwar da ake fama da ita a kasar.

Ma’aikata da dama a Amurka sun fada halin kaka-ni-ka-yi na matsin tattalin arziki, musamman ma lokacin da annobar COVID-19 take kan ganiyarta.

Babbar bukatar malaman dai ita ce ta kara mafi karancin albashinsu zuwa Dala 54,000 a shekara, kwatankwacin sama da Naira miliyan uku, sannan a inganta walwalarsu.

Bugu da kari, malaman na neman a kara inganta yanayin aikin nasu sannan a ba masu bukata ta musamman da dalibai da yara kulawa ta musamman.