✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin bayani kan maganar fyade a gidan aure!

Wadansu matan aure na fadawa fasikanci a dalilin rashin kula da ibadar aure.

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko:

Al’amarin da ban mamaki irin yadda wannan fili yake ci gaba da samun korafi daga masu karatu kan lallai sai an gyara bayanin da ya gabata, suna son a nuna cewa ya halatta miji ya rika yi wa matarsa fyade a duk lokacin da ya so.

Wai a cewarsu, hakan shi ne daidai da Sunnar Manzon Allah (SAW).

Amma kuma in muka bibiyi Sunnar Fiyayyen Halitta (SAW) za mu ga cewa wannan ya yi kishiya da abin da ya aikata ko ya koyar ko ya umarta.

Don haka, masu wannan batu sai su je su nemi ilimin addini don su gyara iliminsu, su daina yi wa addinin Musulunci gurguwar fahimta.

Sannan wadansu suna ganin halin isgilanci irin na ’ya mace shi yake sa mijin ya nemi bukatarsa ta karfin tsiya ko ta ki ko ta so, misali:

Tambaya: Anty Nabila na ji bayaninki a kan fyade a gidan aure. To tambaya a nan ita ce a cikin matan wannan zamani akwai wacce take wata biyar ma ana kai ruwa-rana da ita a kan hakkin aure kuma wallahi lafiyarta kallau.

Kawai tsabar iskanci ne, dalilin haka maza da yawa sun shiga neman matan banza.

Amsa: Duk macen da take yi wa mijinta kiyo ko wani abu na rashin ladabi da girmamawa, to, akwai hanyoyin da shari’a ta tanada da zai bi don ya ladabtar da ita, ya yi mata saiti.

Amma yin ibadar aure da karfin tsiya ba shi ne mafita ba, don wannan zai iya sa tsana mai karfin gaske a zuciyar matar da rashin son ibadar auren, wanda hakan zai kara dagula zamantakewar auren ne gaba daya.

Da yawan magidanta suna kuskuren rashin yin la’akari da cewa akwai fadi mai girman gaske a tsakanin sha’awar mace da ta namiji musamman a fannin jin tsunkulin sha’awa da kuma kasancewa cikin son kusantar abokin aure.

Ita mace ’yar shauki ce, shauki ya fi karfi a cikin ma’aikatar hankalinta, don haka in ba ka nuna mata kyawawan shau’uka a zuciyar matarka game da kai da kuma zamantakewarku ba, hakan yana iya haifar da matsalar ibadar aure a tsakaninku.

Domin muddin zuciyarta babu kyakkyawan tunani game da kai, to ko an yi ibadar aure za a ji ta kadas ne kawai.

Maza na da makullin bude sha’awar ’ya mace a hannunku, kyakykyawar zamantakewarku gare su ce mabudin sha’awarsu, yawan yabo, kodawa da wasa da dariya shi ne makunnin sha’awarsu, sannan kyautatawa za ta sa mace ta wadata mijinta da jikinta a duk lokacin da ya so.

Ku yi la’akari da yadda Allah Madaukakin Sarki Yake ta yawan maimaita kyautawawa a duk wani al’amari na game da mata cikin rayuwar aure, saboda da kyautatawar ce za ku same su yadda kuke so da kyautatawar ce za ku ci moriyarsu fiye da yadda suke cin taku.

Kamar yadda mai tambaya ya nuna cewa wata sai an yi wata biyar ba tare da ta bari mijinta ya kusance ta ba, wannan shi ne dalilin da mijin yake neman sha’awarsa ta hanyar karfi, to akwai matan da su ma mijinsu bai kusantarsu da ibadar aure na tsawon watanni duk da cewa suna cikin tsananin bukata.

To su ma sai su yi fyade ga mijinsu ke nan su nemi biyan bukatarsu da karfin tsiya?

Auren nan fa don morewar mata da miji aka yi shi, ba don maza kadai ba, biyan bukatar sha’awa duka abokan aure suna da muhimmanci ba wai ta maigida kadai ke da muhimmanci ba.

Su ma matan aure wadansu suna fadawa fasikanci a dalilin mazansu ba sa kula su da ibadar aure. Don haka, ba a gyara barna da wata barnar.

Tambaya: Mun ji laifin mai fyade saura kuma a fada mana laifin da mace in ta yi wa mijinta ya yi daidai da fyade, ko ita ba ta da laifi ne saboda ita mace ce?

Amsa: Kwarai kuwa matan aure suna laifi sosai, hana ibadar aure ba da wani kwakkwaran dalili ba.

Babban laifi ne kuma in kana biye da wannan fili ka san mun sha yin bayanan nasiha da tsoratar ga matan aure game da wannan al’amari.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance a cikin kulawarsa a koyaushe, amin.