✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karnuka sun ceto jaririyar da aka yasar tare da dumama mata jiki

Dole ne in ce, jaririyar ’ya ce mai sa’a.

Wata jaririya da aka yasar a Lardin Chattisgarh ta kasar Indiya, ta samu ceto bayan da wani kare da ’yan uwansa suka same ta a kwance, suka taimaka mata inda suka ajiye ta a wajensu.

Jaririyar da aka sanya wa suna Akanksha, rahoto ya ce bayan daukar jaririyar da karnukan suka yi sun rufe ta da jikinsu don ba ta dumi har zuwa wayewar gari lokacin da aka karbe ta daga hannunsu.

’Ya’yan kwiya-kwiyan sun rufe ta don ta ji dumi tare da kauce wa sanyi a cikin dare.

Jaririyar ta hadu da bakin ciki kan rashin tausayi daga wadanda suka yasar da ita a cikin dare, ba tare da sutura ba kuma ba a yanke mata cibiya ba.

Rahotanni sun ce, wani kare ne ya gano jaririyar inda ya lullube ta tare da ’ya’yansa har wayewar gari a Lardin Chattisgarh.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Watakila dumin da jaririyar ta samu daga ’yan kwiya-kwiyan da mahaifiyarsu ne ya taimaka mata, har ta rayu zuwa wayewar gari.

“Yawanci akan yi fama da sanyi da daddare musamman a cikin watan Disamba.

“Dole ne in ce, jaririyar ’ya ce mai sa’a.”

An gano jaririyar tare da sauran ’yan kwiya-kwiyan, yayin da jaririyar ba ta ji wani rauni ba kuma an gano ta ce bayan mazauna yankin sun ji kukanta.

Mutane sun sanar da jami’an gwamnati da ke yankin, daga nan aka tuntubi ’yan sanda.

An mika jaririyar ga cibiyar kula da lafiyar yara ta kasar bayan likitoci sun duba ta a wani asibiti da ke yankin.

Daya daga cikin mazauna yankin, Premnath, ya ce “Abin al’ajabi ne da jaririyar ta tsira da daddare daga karnukan, saboda karnukan suna iya kashe ta, musamman da yake su ma bas u da gida,” inji shi.

Ya ce: “Ba karnukan da suke da gida ba ne, karnuka ne masu yi wa jama’a barna.

“Abin al’ajabi ne a samu jaririyar da aka haifa a raye a lokacin da karnukan da suke gararamba wadanda suke farautar matattu ko rayayyun halittu don yin kalace.”

An radawa jaririyar suna: Akanksha Ana ci gaba da bincike, kuma ’yan sanda na neman iyayen jaririyar.

Babban jami’in ’yan sandan Chhattisgarh, Darakta Janar na musamman RK Bij ya bayyana kaduwarsa a kan lamarin.

Bayan faruwar lamarin, wani wakilin yankin mai suna Munnalal Patel ya ce, sun samu jaririyar ce bayan sun fita ayyukan yau da kullum.

Ya ce: “Da karfe 11:00 na safe, sai muka tsinci jaririyar sabuwar haihuwa tana kuka tana kwance tare da ’yan kwiya-kwiyan a kauyenmu.

Patel ya ce, “Mun firgita muka sanar da ma’aikatan lafiya kafin a kai jaririyar asibiti domin a duba lafiyarta.