✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KAROTA ta kama mota cike da barasa a Kano

Hukumar KAROTA ta bankado wani sabon salo da direbobi suka kirkira wajen shigo da barasa cikin Jihar Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta cafke wata mota kirar Canta da ta dauko giya kwalba 4,600.

Shugaban Hukumar KAROTA, Faisal Mahmud Kabir ne ya sanar da hakan a lokacin da yake sanar da cewa hukumar bankado wani sabon salon da direbobi suka kirkira wajen shigo da giya jihar.

Jami’an da suka cafke motar sun bayyana cewa a lokacin da suka tsayar da motar, direban ya shaida musu cewa itacen girki ya dauko.

Amma bayan da aka matsa da bincike sai aka fahimci ba itacen ba ne, barasa ce a ciki.

Shugaba Hukumar ya ce da zarar an kammala bincike za a mika giyar ga Hukumar Hisbah domin fadada bincike da daukar mataki na gaba.