✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaso 70 Na Fursunonin Kano Jiran Shari’a Suke Yi

Hukumar gidajen yari ta Najeriya (NCoS) reshen jihar Kano, ta ce, kashi 70 cikin 100 na fursunonin jihar zaman jiran shari’a  suke yi a gidajen…

Hukumar gidajen yari ta Najeriya (NCoS) reshen jihar Kano, ta ce, kashi 70 cikin 100 na fursunonin jihar zaman jiran shari’a  suke yi a gidajen yarin  da ake tsare da su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito kakakin hukumar a jihar, SC Musbahu Lawan yana cewa cunkoson  fursunonin ya zama kalubale ga yadda Hukumar ke gudanar da ayyukanta a jihar.

Lawan ya ce  yawan fursunonin da ke jiran shari’a ya ninka na wadanda aka yanke wa hukunci sau uku a gidajen yarin jihar.

“Alkaluma sun nuna kashi 30 na fursunonin ne kawai ake yanke wa hukunci , yayin da  kashi 70 na fursunonin ke zaman jiran shari’a.

“Yawancin fursunonin da ke jiran shari’a suna gidajen yarin ne a cikin yanayi na rashin tabbas.

“Dokokinmu sun ba mu damar tura fursunonin da aka yanke musu hukunci zuwa kowane gidan yari a Najeriya.

“Don haka idan aka yanke wa fursunonin da ke jiran shari’a hukunci za a samu sukin cunkoso, domin za mu iya tura su wasu jihohin.”

Ya yi nuni da cewa fursunonin da aka yanke wa hukuncin sun fi saukin gudanar da su domin an ba su damar shiga shirye-shiryen gyara daban-daban.

“Yawancin fursunonin da aka yanke musu hukunci kuma suna amfana da shirye-shiryen ilimi a wuraren da ake tsare da su.
“A Kano, fursunoni 38 da aka yanke wa hukunci sun yi jarabawar kammala sakandare kuma yanzu suna neman gurbin karatu a  Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN).

“Saboda karuwar sha’awar yin karatu a tsakanin fursunonin, muna kokarin hada kai da NOUN domin kafa ƙarin cibiyoyin karatu a gidajen yari,”

Ya ce daya daga cikin kalubalen da shirin ke fuskanta shi ne rashin wuraren karatu masu inganci da kuma kayyakin karatu.