✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan dalibai: Gwamnati ta ce Yobe ba ta da niyyar sake rufe makarantun jihar

Gwamnatin  jahar Yobe ta bayyana cewa babu wani shiri da take da shi na sake rufe makarantun sakandare da Firamaren jahar a bisa abin da…

 Dalibai biyu da abin ya shafa a kwance a gadon asibitin DamaturuGwamnatin  jahar Yobe ta bayyana cewa babu wani shiri da take da shi na sake rufe makarantun sakandare da Firamaren jahar a bisa abin da ya faru na harin da wadansu ‘yan bindiga suka ka kwalejin nazarin aikin noma ta Gujba wadda ya yi sanadiyar rasa rayukan dalibai sama da 50.
 Bayanin hakan ya fito ne daga kakakin gwamnan jahar Alhaji Abdullahi Bego a lokacin da yake bayani ga manema labarai a garin Damaturu dangane da rade-radin da wadansu ke bazawa na yiwuwar sake rufe makarantun  jahar da ba su wuce makoni biyu ba da sake bude su ba.
 Alhaji Abdullahi Bego ya kara da cewa, hobbasan da gwamnatin ke yi a yanzu shi ne hada hannu da jami’an tsaron jahar don ganin an samar da tsaro mai inganci a makarantun jahar kamar yadda gwamnatin ta fada a baya kafin ma a bude makarantun.
 Don haka ne, a cewar kakakin na gwamna, gwamnatin jahar ta nemi jami’an tsaron da ke da ruwa da tsaki dangane da kula da harkokin tsaron jahar da su sake shiri don ganin sun samar da kyakkyawan tsaro a dukanin makarantun jahar don kauce wa sake faruwar irin haka.
 Ya kuma tabbatar wa al’ummar jahar cewa gwamnatin jahar ta yi bakin cikin faruwar wannan ta’addanci da aka aiwatar a kan daliban da ba su ji ba ba su gani ba. Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Yobe ta shirya domin bayar da duk wani taimako ga jami’an tsaron don ganin an kai ga biyan bukata na samar da cikakken tsaro ga makarantun.
Idan za a iya tunawa kasa da makonni biyu ke nan da gwamnatin jahar Yobe ta bada umarni ga dukannin makarantun sakandare da Firamare da ke jahar da su bude makarantun nasu don fara gudanar da karatu a sabuwar shekarar karatu ta bana 2013/2014 tare da kiran iyaye da su tura yaransu makarantun sakamakon jinkirin makonni biyu da aka samu na bude makarantun, kamar yadda kalanadar karatu ta makarantu ta nuna, sai ga shi kwatsam wadansu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki a kwalejin nazarin aikin noma da ke garin Gujba inda suka halaka dalibai sama da 50, tare da jikata akalla 18 daga cikinsu.
 Kamar yadda shugaban kwalejin aikin noman Malam Murima Maimato Gaidam ya bayyana, ya ce wannan harid na ‘yan bindigan da suka kai da tsakar daren ranar lahadi ya yi sanadiyar rasa rayukan dalibai sama da 50, kuma ‘yan bindigar sun shiga dakunan kwanan daliban ne suka rika harbin kan mai uwa da wabi.
 Jami’an tsaro suna kokarin kai wadanda suka jikkata asibiti.Wata majiya kuma a makarantar ta shaida wa Aminiya cewa wadannan ‘yan bindiga sun zo ne cikin kwambar motoci kimanin uku tare da Babura, kuma suna da matukar yawa, daga zuwan sai suka rika tara daliban a wani babban dakin kwanansu inda a nan ne suka rika bude musu wuta babu kakkautawa,  a yayin da wadansu daliban suka samu nasarar tserewa zuwa cikin daji, tun da makaranatar a gab da daji take. Majiyar ta ce sun shafe sama da sa’o’i uku suna cin karensu babu babbaka a cikin wannan makaranta ba  tare da fuskanatar wani kalubale daga jamian tsaron da ke kai kawo a yankin ba.
 Wani dalibi da ya sha da kyar amma tare da harbin bindiga a jikinsa mai suna Bello Muhammad Hassan, ya shaida wa Aminiya cewa shi ma Allah (SWT) ne Ya cece shi da shi ma a yanzu sai dai labari, domin kuwa su 15 ne  a dakinsu lokacin da ‘yan bindigan suka zo suka bude musu wuta, sai kawai ya fado a kan gadonsa lokacin da suka harbe shi a gab da mahadar wuyansa ta kasa amma sai ya gangara kasar gado ya yi lif, suna tsammani ko ya mutu ne, sai suka bar shi suka fita, kasancewar duk sun harbe ‘yan uwansa.
 Aminiya ta tarar da mahaifin wani dalibi da bai amince ya fadi sunansa ba. yana neman yaronsa a cikin gawawwakin daliban da aka kashe amma bai gan shi ba, bai kuma samu labarinsa ba, inda ya shaida wa Aminiya a dimauce cewa shi babu wanda ya dora wa laifin wannnan lalata da aka yi wa yaransu sai gwamnati, domin tun da ta san ba ta shirya kare raukan yaransu ba don me za ta ba da umarnin  su koma makaranta?
 Don haka malamin ya bukaci gwamnatin jahar Yobe da ta fito ta bayani ga iyayen daliban jahar domin gamsar da su, idan ba haka ba shi da wadansu iyayen yaran za su cire yaransu daga makarantun jahar don nema musu makarantu a wadansu jahohin da za a iya kare lafiyarsu.
 dimbin gawawwakin daliban da aka kai babban asibitin garin Damaturu ya sa mutanen da suka yi cincirin don jimamin wannan ta’asa fashewa da kuka. A wannan lokacin wani yamutsi ya so ya tashi a sakamakon wata barambarama da wani jami’in ‘yan sanda ya yi a wurin, inda ya ce a lokacin da ake kashe ‘yan sanda ai mutane murna suke yi, to yau ga shi abin ya dawo kansu, wannan Magana c eta bata wa mutanen da ke wurin rai har suka nema taba lafiyarsa said a ‘yan uwansa jami’an tsaro suka cece shi.  
Kakakin rundunar tsaro ta 3 da ke jahar Yobe Kaftin Eli Lazarus ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya yi karin haske da cewa ‘yan bbindigar sun kai wannan mummunan farmakin nasu ne da tsakar dare wajen karfe daya inda suka kashe dalibai sama da 50 tare da ji wa wadansu raunuka, sun kuma zo ne a cikin motoci kiran Toyota Hilud da kuma Golf, suka kuma tsere da wata motar daukar marasa lafiya ta makarantar.
 Kaftin Lazarus ya kuma bayar da tabbacin cewa jami’an tsaro na nan suna bin diddigin wadannan ‘yan ta’adda har sai sun cafko su don su fuskanci hukunci. Ya kuma yi fatan al’umm za su ci gaba da ba su hadin kai don tona asirin bata-gari.
 A lokacin da ya ziyararci babbamn asibitin na Damaturu don duba gawawwakin daliban da kuma wadanda aka jikkata, Gwamna Ibrahim Gaidam na jahar Yobe, wanda ya katse ayyukansa a Abuja ya dawo don fuskantar wannan lamarn,i ya bayyana matukar damuwarsa dangane da faruwar wannan abu tare da yin Allah wadai ga wadannan ‘yan bindiga, ya ce wannan babban ta’addanci ne kuma da yardar Allah sai asirin wadannan ‘yan ta’adda ya tonu.
Yan uwa da abokan arziki lokacin da suka taru don gano gawarwakin ‘yan uwansu a dakin ajiye gawarwaki na asibiti.   Gwamnan Gaidam ya kuma ba da umarnin da a bai wa wadanda suka ji raunuka magani kyauta har sai sun samun sauki. Ya kuma kalubalanci jami’an tsaro su mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro maimakon yin dogon turanci, domin kafin gwamnati ta sake bude makarantun sai da ta tuntube jami’an tsaro suka ce babu komai.
 Ya kuma shawarci shugaban kasa da ya sake dabara dangane da tsare rayukan al’ummomin jahohin Borno da Yobe saboda halin da suke ciki.