✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Hanifa dabbanci da rashin imani ne —Atiku

Wannan dabbanci da rashin imani ne.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa bisa kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa wata yarinya ’yar shekara 5 mai suna Hanifa Abubakar a Jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a makon jiya, Atiku ya kwatanta lamarin a matsayin “mummunan labari.”

“InnalilLahi wa inna ilayHi raji’un. Na samu mummunan labarin kisan gilla ga yarinya Hanifa ’yar shekaru 5, wadda aka kashe bayan kwashe kwanaki 47 a hannun masu garkuwa.

“Wannan dabbanci da rashin imani ne. Na kasa fahimtar yadda mutum mai hankali zai raba yarinya karama da iyayenta sannan daga bisani kuma ya kashe ta,” a cewar sakon da Atiku a wallafa a shafinsa na Facebook.

Atiku ya kuma mika sakon jajensa tare da yin ta’aziyya ga iyalan Hanifa yana mai kira da a bi mata kadinta.

“Ina kira ga mahukunta da su tabbatar (masu garkuwar) sun fuskanci hukunci.”

A ranar 4 ga watan Disambar 2021, malamin yarinyar mai suna Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita inda ya kai ta gidansa ya ajiye ta har tsawon mako biyu kafin daga bisani ya kashe ta.

Kamar yadda ya fadawa jami’an tsaro, malam Tanko ya ce ya yanke shawarar kashe dalibar ta sa ne bayan da ya yi tsammanin cewa an gano shi ne ya sace ta.