✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami na farko a 2022

Makaman sun yi tafiyar kusan kilomita 500 kafin su fada teku.

A karo na farko bayan shiga sabuwar shekara, kasar Koriya ta Arewa tayi gwajin wasu makamai da ake kyautata zaton masu linzami ne a gabar tekun da ke Gabashin kasar.

Jami’an tsaron gabar ruwan kasar Japan, wadanda suka fara sanar da harba makaman sun ce akwai yiwuwar makaman su kasance masu linzami ne, ko da yake ba su yi cikakken bayani a kan haka ba.

Firaiministan Japan, Fumio Kishida, ya shaida wa manemna labarai cewa, “Tun bara Koriya ta Arewa take ta yin gwajin makamai masu linzami, wannan abin takaici ne matuka.”

Ministan Tsaron Japan, Nobuo Kishi, ya ce makaman sun yi tafiyar kusan kilomita 500 kafin su fada wajen wani sashen kasuwanci da ke iyakar kasar ta Japan.

Kazalika, su ma Manyan Hafsoshin Tsaron Koriya ta Kudu, sun ce an harba makaman ne daga Gabashin kasar da misalin karfe 8:10 na safiya daga kasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya rawaito.

Gwajin dai na zuwa ne ’yan kwanaki bayan kammala babban taron jam’iyyar kasar da ya mayar da hankali a kan farfado da tattalin arzikin kasar wanda annobar COVID-19 ta yi wa illa.

Sai dai Shugaba Kim Jong Un ya yi alkawarin ci gaba da gwada karfin kasar ta hanyar gwajin makaman, ko da yake bai bayyana nau’insu ba.

A bara dai, kasar ta gudanar da gwaje-gwaje da dama, kuma a watan Oktoba, ta gwada wani makami mai linzami da ta yi wa lakabi da ‘Sabon samfuri’, kuma shi ne gwaji irinsa na farko tun shekarar 2019.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta haramta wa kasar gwajin makaman masu linzami karkashin sabbin dokokinta.