✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin mutumin da ‘ya yi ‘garkuwa’ da ’yar cikin sa

Kotun ta ba da belin mutumin da ake zargi, sannan aka dage zama zuwa wani lokaci.

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Sansanin Alhazai na Kano ta ba da belin mutumin da ake zargi da yin garkuwa da diyarsa mai shekara hudu tare da neman kudin fansa daga matarsa.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin a lokacin da aka karanto tuhumar da ake yi masa.

Alkalin kotun, Sakina Aminu ta nemi wanda ake tuhumar ya kawo mutum biyu su tsaya masa daga cikin mutanen gari da kuma limami.

Daga nan ta dage zaman zuwa ranar 9 ga Disamba, 2020 don ci gaba da sauraron shari’ar.

A kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa mahaifiyar yarinyar ta kai kara ga ’yan sanda cewa an sace diyarta a ranar 29 ga watan Satumba kuma aka kira ta a waya ana neman ta biya Naira miliyan biyu kudin fansa ko a kashe ta yarinyar.

Bayan bincike ’yan sanda sun gano cewa mijinta kuma mahaifin yarinyar ne ke kiran ta kuma daga baya aka samu yarinyar da aka sace a tare da shi.