✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin Naziru Sarkin Waka

Fitaccen mawakin nan na Kano, Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya shaki iskar 'yanci bayan da aka sako shi daga…

Fitaccen mawakin nan na Kano, Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya shaki iskar ‘yanci bayan da aka sako shi daga gidan yari inda ya shafe kusan kwanaki biyu a kulle.

An sake kulle Sarkin Wakar ne biyo bayan sakin wasu wakoki biyu ba tare da izinin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ba.

Lauyan da yake kare Nazirun,Tajudeen Abdullahi, ya shaidawa Aminiya cewa sun samu nasarar samun belins nasa ne bayan cika sharuddan da kotu ta gindaya masa.

Idan za a iya tunawa dai gwamnatin jihar Kano ta kama mawakin ne bisa sakin wakokinsa masu taken ‘Gidan Sarauta’ da ‘Sai Hakuri’ ba bisa ka’ida ba wanda hakan ta ce ya saba wa dokar Hukumar Tace Fina-finai ta shekara 2001, karkashin sashi na 100 (2).

Alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari ya bada belin mawakin biyo bayan cin tararsa da aka yi ta kudi Naira miliyan biyu tare da gabatar da mahafinsa ko wani shakiki nasa da kuma kawo daya daga cikin Kwamandojin Hisbah daga kananan hukumomi 44 dake jihar Kano a matsayin wanda zai tsaya masa.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Laraba, Naziru ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi na sakin wakokin ba bisa ka’ida ba.