✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin tsohon Ministan Lantarki Olu Agunloye

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye kan kuɗi naira miliyan 50.

Da yake yanke hukunci a yau Alhamis, mai shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun, ya buƙaci tsohon ministan da ya gabatar da mutane biyu waɗanda za su tsaya masa.

Mai shari’ar ya ce dole ne mutanen da za su tsaya wa tsohon ministan su kasance masu hannu da shuni waɗanda kuma ke zaune a Abuja.

Ya ce tilas ne kuma su mallaki kadarorin da ya kai Naira miliyan 300 tare da takardar shaidar zama wanda za a iya tantancewa.

“Dole ne kuma su miƙa kwafin katin shaidarsu da kwafin fasfo ɗin su na ƙasashen waje ga kotu,” in ji Onwuegbuzie.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu.

An dai gurfanar da Agunloye ne a gaban kotun a ranar Laraba bisa zargin almundanar kuɗi da ya kai dala biliyan shida a badaƙalar kwangilar tashar samar da wutar lantarki ta Mambila.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ce ta gurfanar da shi a gaban kotun, inda tsohon ministan ya yi biris da laifin da ake tuhumarsa.

An gurfanar da tsohon ministan kan tuhume-tuhume bakwai da ke da alaka da tafka almundahana wajen ba da kwangilar da kuma karbar sama da miliyan uku a matsayin na-goro.

Bayan an karanta tuhume-tuhumen ne tsohon ministan ya musanta zargin da aka yi masa yana mai cewa bai aikata laifi ba.

Sai dai bayan sauraron martanin lauyn masu kara da masu karewa, alkalin kotun ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje, har zuwa lokacin da za a bayar da belinsa.

Ana iya tuna cewa, a watan Disambar 2023 ne EFCC ta bayyana Agunloye a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin almundahana.

A cikin sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X (Twitter), ta sanya hoton tsohon ministan tare da yin kira ga jama’a da su ba da bayanan da za su kai ga kama shi.

An dade ana rikici a kotu kan kwangilar da aka fara bayarwa a shekarar 2003 lokacin mulkin tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo.