✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bada umarnin a saki Sanusi II

Wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin a saki tubabben Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da ke zaman hijira garin Awe a…

Wata Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin a saki tubabben Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da ke zaman hijira garin Awe a jihar Nasarawa.

Mai shari’a Anwuli Chikere, ne ya sanar da hakan ranar Juma’a, bayan shigar da karar da lauyoyin Sanusi II, suka yi gaban kotun wanda Alkali Lateef Fagbemi (SAN ) ke jagoranta.

Kotun ta sanar da ranar 26 ga Maris 2020, don ci gaba da sauraran shari’ar.

Kotu ta kuma umarci Sufeton Janar ‘yan Sandan Najeriya da shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS da sauran masu hannu a tsare tsohon Sarki Muhammadu Sunusi na II da su sake shi.