✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda

An shardanta wa Danbilki kwamanda ya kawo hakimi da Babban Sakatare a wata ma'aikata gwamnati

Kotun Majistare ta ba da belin fitaccen dan Jam’iyyar APC a Kano, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, wanda ake zargi da neman tayar da zaune tsaye a jihar.

Kotun da ke zamanta a Normanslan, karkashin jagorancin Mai shari’a Abdul’aziz Habib, ta shardanta wa Danbilki Kwamanda ya kawo Babban Sakatare a wata ma’aikata a Jihar Kano ko kuma hakimi su tsaya masa.

Hakazalika dole ne wanda ake kara da wanda zai tsaya masa su mika wa kotu fasfunansu na tafiye-tafiye.

Kotun ta sanya ranar 26 ga watan Fabreru don ci gaba da sauraren shariar.

A ranar 23 ga  Janairu aka fara gurfanar da Danbilki Kwamanda bisa zargin sa furta kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye dangane da masarautun jihar a lokacin da yake hira a wani gidan rediyo da ke jihar.

Mai gabatar da kara Barista Bashir Saleh ya shaida wa kotun cewa hakan ya saba da sashe na 114 a Kundin Sharia Pinal Kod.

Sai dai wanda ake karar ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa, dalilin da lauyansa, Barista Ibrahim Chedi ya nemi kotun ta bayar da belinsa.

Sai dai kotun ba ta bayar da belinsa a wancan lokaci ba, ta tsare shi a gidan gyaran hali tare da dage shariar zuwa ranar 29 ga Janairu don yanke hukunci a kan batun belin nasa.

A ranar 29 kuma kotun ba ta zauna ba sakamakon rashin lafiyar Alkalin Kotun inda aka dage shariar zuwa yau 1 ga watan Fabreru 2024.