✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci tarar ’yan kallon shari’ar wanda ya saci abincin makwabcinsa

Alkali ya yi wa wanda aka kai kara kan satar dafaffen abincin makwabinsa kyautar kudin shari'ar da mai karar ya biya da kuma tarar da…

Wani mutum ya makwabcinsa kotun saboda zargin dibar amsa dafaffen abinci a garin Dirin Daji a Jihar Kebbi.

Wani mazaunin garin da ya yi wa Aminiya bayanin irin yadda kitimurmurar ta faru tsakanin magidancin da makwabcinsa, da kuma yadda karshe ciko ya biyo gyartai.

Shaidan namu a garin mai suna Murtadha Faruk Sale ya ce, “Ka san wannan matsalar ta rayuwa da aka shiga yawanci mutanen babu abinci, sai ka samu wasu iyalan an kwana uku koma fiye ba a dora girki ba.

“Shi wannan, ’ya’yansa suna masa kukan yunwa suke ji, da su ci abinci ba, shi kuma wannan mutumin sai ya yanke shawarar bari ya je wurin makwabcinsa ya nemi ya taimaka masa da abin da zai ba yaran suci tun da yunwa suke Ji suna ta kuka,” in ji shi.

Murtadha Faruk Sale ya ci gaba da cewa “ko da yaje gidan makwabcin nasa sai ya tarar ba ya nan, ya samu matar tana abinci a zaure, ko da ya yi sallama sai matar ta ce mai gidan ba ya nan.

“Ashe bai tafi ba, ya labe a zauren, dama ya tafi da kwano. Ko da matar maigidan ta shiga cikin gida daukar wani abu, sai ya sa kwanon ya debi abinci ya kai wa ’ya’yansa suka ci.

“Maigidan na dawowa sai matar ta sanarwa mijin ga abin da ya faru, shi kuma mutumin ya kai maƙwabcin nasa ƙara a gaban kotu inda ya nemi alƙali ya ɗaure shi saboda ya satar masa dafaffen abinci ya kai wa ’ya’yansa.

“Sa allƙalin kotun ya tambayi wanda ake ƙara ko me ya sa ya aikata wannan aiki sai ya ce, ‘kwana da kwanaki ba a iya ɗora tukunya a gidana, kuma ya san halin da nake ciki.

“‘Na nemi ya taimaka min ko da bashi ne ya ranta min idan aikin kaka ya zo na yi aikin gona in biya shi, amma ya ƙiya, ni kuma na fakaici idon matarsa, dama a cikin zaure take yin girki, ina fitowa waje naga ta tashi, sai na lallaɓa na kamfato abincin na kai wa yarana, don sun dame ni da kukan yunwa, kuma babu inda ban buga ba don in nemi abinci na rasa, babu aikin yi’.

“Nan take alƙalin ya ce wanda yake ƙarar ya kawo dubu 30 kuɗin shari’a don a yanke hukunci, ya sa hannu aljihu ya ƙirgo ya bada.

“Alƙalin ya sauko da kansa ya amshi kuɗin ya je ya damƙa wa wanda ake ƙara, ya ce ga shi nan kaje ka ƙara saya wa ’ya’yanka abinci.

“Sannan alƙalin ya umarci ma’aikatan kotun su rufe ƙofa, duk wanda ya zo kallon shari’ar sai ya yi belin kansa a kan Naira 1,000, alƙali ya ciro nasa dubu ɗayan ya ce ga tashi ya fara ajewa.

“Ana gama haɗa kuɗin sai alƙalin ya tattara su duka ya sake damƙa wa wanda ake ƙara, kuma ya ce ya kori shari’ar nan take.