✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Kotu ta daure mai gadi kan yi wa ‘yar shekara bakwai fyade

Ya yi wa yarinyar fyade da karfin tsiya a lokacin da ta fito yin fitsari a cikin dare

Wata kotun Majistare da ke zama a Igarra ta Jihar Edo ta daure wani mutum shekara 9 saboda laifin yi wa yarinya ‘yar bakwai fyade.

Kotun ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 hukuncin bayan samun sa da yi wa yarinyar fyade a ranar 19 ga watan Agustan 2019.

A baya an yi ta dage sauraron sha’ar’ar kafin daga bisani a yanke hukuncin a ranar Laraba makon jiya.

Mai shigar da karar, Obaze Samuel ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar yana gadi ne a unguwar da yarinyar take, ya kuma aikata laifin ne cikin dare a lokacin da yarinyar ta fito daga gida domin ta yi fitsari.

Ya ce wanda ake zargin ya yi lalata da yarinyar wanda ya saba sashe na 218 na dokar manyan laifuka ta kasa.

Alkalin kotun Mai Shari’a Nosa Musoe ta tabbatar da tuhumar da ake yi wa mai gadin.

Ta ce hujjojin tuhumarsa a bayyane suke don haka ta yanke masa hukuncin daurin shekaru tara cikin aikin wahala ba tare da ta ba shi zabin tara ba.

Alkalin kotun ta ba da umarnin tisa keyar mai laifin zuwa gidan gyara halinka da ke birnin Auchi a jihar Edo.