✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure tsohon Darektan NIMASA Agaba shekara bakwai

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta yanke hukuncin daurin shekara bakwai a kan tsohon Babban Darektan Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Ruwa…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta yanke hukuncin daurin shekara bakwai a kan tsohon Babban Darektan Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Ruwa da Lafiyar Teku ta Najeriya (NIMASA), Ezekiel Agaba bayan kama shi da laifin zambar biliyan N1.5.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Mai Shari’a Ibrahim Buba ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayar da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da Ezekiel Agaba ya aikata laifin da ake tuhumarsa.

A shekarar 2015 ne EFCC ta fara gurfanar da tsohon Babban Darektan tare da tsohon Darekta Janar na NIMASA Patrick Akpobolkemi da wasu mutun biyu bisa zargin karkatar da biliyan N2.6 da hukumar ta ware domin aiwatar da shirin tsaron jiragen ruwa da teku (ISPS).

EFCC ta ce dokar ISPS ta tanadi tabbatar da lafiya da tsaron jiragen ruwa kasa da kasa da ke shigowa Najeriya.

Tuni kotun ta sallami Akpobolokemi, yayin da EFCC ta janye tuhumar da take wa sauran mutum biyun, ta bar Agaba.