✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana Timipre Sylva tsayawa takarar gwamnan Baylesa

Duk da hukuncin kotun, APC ta ce kamar Sylva ya ci zaben ya gama, kuma shi za a rantsar

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana tsohon Gwamnan Beyelsa Timipre Sylva fitowa takarar kujerar gwamnan jihar, wata guda kafin zabe.

Sai dai jam’iyyarsa ta APC ta ce kamar Timipre ya ci zaben ya gama, kuma shi za a rantsar a watan Fabrairu a matsayin gwamnan jihar.

A ranar Litinin kotun ta taka burki ga tsohon karamin ministan man fetur din, wanda shi ne dan takarar gwamnan Jam’iyyar APC a zaben da ke tafe ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya bayyana cewa kundin tsarin mulki na 1999 bai ba wa Sylva damar yin takara ba, saboda an taba rantsar da shi sau biyu a matsayin gwamna inda ya yi mulki na tsawon  shekaru biyar.

Alkalin ya ci gaba da cewa idan dan takarar na APC ya ci zabe da ke tafe, za a rantsar da shi a karo na uku ke nan, sannan idan ya yi wa’adinsa na shekaru hudu zai zarce shekara takwas da kundin tsarin mulki ya amince.

Don haka ya ce tsohon gwamnan bai cancanci yin takara a zaben ba saboda idan ya ci zaben, abin da zai biyo baya zai ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da APC ta yi ikirarin cewa babu baraka a cikin gidanta, gabannin zaben na Gwamnan Bayelsa, kuma masu ruwa da tsaki sun ce a shirye suke domin ganin Sylva ya kai bantensa a zaben kuma an rantsar da shi wa watan Fabrairun 2024.