✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta raba auren shekara 14 saboda rashin kulawa

Mijin ya ce ya guji iyalan nasa ne sakamon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano, ta raba auren wasu ma’aurata da suka shafe shekara 14 da aure sakamakon rashin kulawa.

Kotun ta raba auren wani direba mai suna Zakari Ghali mai shekara 48 da matarsa Shamsiyya Haruna mai shekara 33, sakamakon yin watsi da al’amuransu.

Matar wadda ke zaune a Unguwa Uku, ta roki kotu da ta raba auren tare da ba ta ikon ‘ya’yansu guda biyar sakamakon watsi da su da mijin ya yi.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Malam Umar Lawal Abubakar, ya ce an raba auren ne bayan gaza sulhunta ma’auratan biyu.

Tun da farko ya umarci Ghali da ya biya wadda ta shigar da karar Naira 90,000 don kula da yaransa duk wata.

Ghali, ya shaida wa kotun cewa ya guje su ne saboda matsalar tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu.

“Ba ni da kudin da zan ciyar da iyalina yanzu. Mai motar da nake amfani da ita wajen safarar kaya ya kwace motarsa,” in ji shi.